Sabbin hotunan El-Rufai inda ya ɗau wankan jins tamkar wani saurayi yayin da ya fita duba wasu ayyukan jiharsa

Sabbin hotunan El-Rufai inda ya ɗau wankan jins tamkar wani saurayi yayin da ya fita duba wasu ayyukan jiharsa

  • Gwamna Nasir El-Rufai ya birge mutanen gari da irin sabuwar wanka da ya dauka a ranar Laraba, 1 ga watan Disambar, lokacin da ya fito duba aiki
  • An hangi gwamnan sanye da riga T- shirt da wando jeansa da kuma takalma trainers wadanda suka dace da irin wankar da ya yi
  • Wannan shigar tasa zai iya bawa wasu mutanen mamaki duba da cewa an saba ganinsa ne a waje da kaftani, jamfa ko babban riga wato shiga irin ta arewa

Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a ranar Laraba, 1 ga watan Disamba, ya fita da kansa domin duba aikin fenti da ake yi a wasu sassan babban gadar Leventis da ke birnin Kaduna.

Gwamna El-Rufai wanda aka saba gani sanye da jamfa ko babban riga duk lokacin da zai fito waje, a yau an gan shi ya koma tamkar matashi.

Kara karanta wannan

Davido ya kashe Naira miliyan 240, ya sayo motar su wane-da-wane, Rolls Royce 2021

Hotunan El-Rufai ya dau wanka tamkar matashi yayin da ya fita duba aikin gada a Kaduna
El-Rufai ya bawa mutane mamaki da sabuwar wanka da ya dauka. Hoto: Kaduna State Governor
Asali: Facebook

Gwamnan na jihar Kaduna ya saka riga T-Shirt na mai launin fari, sai wanda jeans mai launin ruwan bula da kuma takalma 'trainers'.

Ya rubuta a shafinsa na Facebook:

"A wannan ranar,
"Wannan gwamnatin,
"Kaduna tana sake mike wa."

Cikaken Jerin Sunayen Malamai 233 Da Gwamnatin Kaduna Ta Kora Kan Satifiket Ɗin Bogi

A wani labarin, kun ji cewa, Mr Tijjani Abdullahi, Shugaban Hukumar Ilimin Bai Daya, ya sanar da cewa za a sallami malamai 233 daga ciki kan zargin gabatar da sakamakon kammala karatu na bogi.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Abdullahi ya ce baya ga korarsu daga aiki, za a kuma maka su a kotu.

Ya ce malaman sun gabatar da satifiket din makarantun da suka hada da Cibiyar Horas da Malamai, NTI, Kwallejin Ilimi ta Zaria, FCE, Kwallejin Nuhu Bamalli, Zaria, Kwallejin Ameer Shehu Idris da Kwallejin Ilimi ta Gidan Waya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel