Hanyoyin da gwamnatin tarayya za ta bi don magance matsalolin tsaro, DSS

Hanyoyin da gwamnatin tarayya za ta bi don magance matsalolin tsaro, DSS

  • Hukumar jami’an tsaro na fararen kaya, DSS ta kawo shawara akan hanyar da gwamnati za ta bi don dawo da zaman lafiya da tsaro a garuruwa
  • Darekta janar na ‘yan sanda fararen kaya, Yusuf Bichi, ya yi wannan bayanin a wani taro na 2021 Ugwumba Enterprise Challenge, ya kawo mafita
  • A cewarsa, samar wa matasa tudun rabewa da kuma shawo kan matsalolin kyarar mata zai kawo zaman lafiya mai dorewa da Najeriya ta cancanta

FCT, Abuja - Hukumar jami’an tsaro na fararen kaya ta DSS, ta ba gwamnatin tarayya shawarwari akan hanyoyin samar da zaman lafiya da tsaro a garuruwa, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaba hukumar ‘yan sandan farin kaya, Yusuf Bichi, wanda ya yi jawabi a taron 2021 Ugwumba Enterprise Challenge, ya ce musamman idan aka mayar da hankali kan matasa da matsalar kyarar mata, Najeriya za ta samu zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Samma-kal: Da mulkin farar hular nan, gara gwamnatin Sojoji inji Ministan Obasanjo

Bichi wanda ya samu wakilcin kakakin DSS, Peter Afunanya, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta hada kai da mutane da kungiyoyin da za su janye hankalin matasa daga tituna don basu abubuwan yi.

Hanyoyin da gwamnatin tarayya za ta bi don magance matsalolin tsaro, DSS
Jami'an hukumar yan sandan farin kaya, DSS. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daily Trust ta ruwaito yadda ya ce abinda Ugwumba Leadership Centre take yi shine tabbatar da matasa sun dogara da kawunansu musamman a bangaren kudi don taimaka wa gwamnati wurin shawo kan rashin tsaro.

Ya ce matsawar aka shawo kan matsalolin matasa da mata an gama da matsalar rashin tsaro

Ma’aikacin DSS din ya ce:

“Idan ka gama da matsalolin matasa ko kuma ka shawo kan matsalar wariya da kyarar mata, ka gama da batun rashin tsaro.
“Misali, kamar yadda muka sani, kasar mu tana fama da rashin tsaro, ba kuma a Najeriya kadai bane, gaba daya duniyar ce, kasashe da dama su na da irin wadannan matsalolin.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Al'amarin ya isa haka, Matasan arewa sun fara yi wa Buhari bore

“Ba yakar ‘yan ta’adda bane kadai zai kawo zaman lafiya. Sai mun tallafa wa matasa da kananun sana’o’i ta hanyar basu damar dogaro da kawunansu.”

Rochas Okorocha ya ce ya kamata matasa su mayar da hankula akan kananun ayyukan da suka tsinci kawunansu

Yayin tattaunawa da manema labarai bayan kammala taron, tsohon gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha, ya hori matasa da su dinga mayar da hankulansu akan abubuwan da suke yi.

Okorocha ya kara da cewa mutum zai iya samun nasara matsawar ya mayar da hankali akan komin kankantar abinda yake yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel