Yanzu-Yanzu: Jirgin sama ya tarwatse da babban hafsan tsaron kasar Indiya

Yanzu-Yanzu: Jirgin sama ya tarwatse da babban hafsan tsaron kasar Indiya

  • A yau Laraba ne aka samu labarin cewa, wani jirgi mai saukar ungulu a kasar Indiya ya fado tare da babban hafsan tsaron kasar
  • Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, an dauki wasu da suka jikkata zuwa asibiti domin duba lafiyarsu
  • Amma ya zuwa yanzu, rahotanni basu bayyana ko babban hafsan tsaron ya jikkata ba a wannan hatsari

Indiya - Wani jirgin sama mai saukar ungulu dauke da babban hafsan tsaron kasar Indiya, Janar Bipin Rawat ya yi hatsari a jihar Tamil Nadu da ke kudancin kasar, in ji rundunar sojin sama.

Rundunar sojojin saman Indiya a shafin Twitter ranar Laraba ta bayyana cewa:

"Wani jirgi mai saukar ungulu na IAF Mi-17V5, tare da CDS Gen Bipin Rawat a cikinsa, ya gamu da hatsari a yau a kusa da Coonoor, Tamil Nadu.

Kara karanta wannan

Rahoton ‘yan sanda: Dalibai biyu sun mutu, 12 sun jikkata a hatsarin babbar mota ranar Talata

Hatsarin jirgin sama da babban hafsan tsaron Indiya
Yanzu-Yanzu: Jirgin sama ya tarwatse da hafsan sojojin kasar Indiya | Hoto: anews.com.tr
Asali: UGC

Rundunar sojin saman ba ta bayyana ko Rawat ya ji rauni a hatsarin ba, AlJazeera ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani mai watsa labarai a kasar Indiya Prasar Bharati ya ce an kai mutane uku da suka jikkata zuwa asibiti.

Hotunan talbijin sun nuna jirgin na ci da wuta yayin da mazauna yankin ke kokarin kashe wutar.

Kawo yanzu dai ba a san musabbabin hatsarin da sauran fasinjojin jirgin ba. CNN ta ruwaito rundunar sojin saman Indiya na cewa:

"An ba da umarnin gudanar da bincike don gano musabbabin hatsarin".

Rawat shi ne babban jami'i a rundunar sojin Indiya kuma mashawarci ga ma'aikatar tsaro. Ya karbi sabon mukamin ne a shekarar bara bayan ritayarsa a matsayin hafsan soji.

Kamfanin dillancin labaran Indiya ya labarta cewa, jirgin mai saukar ungulu na Mi-17V5 na kan hanyarsa ne daga sansanin sojin sama zuwa kwalejin tsaron soji a lokacin da ya fado kusa da Coonoor a jihar Tamil Nadu.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya yiwa sojojin da suka raunata a yaki da ISWAP abin alheri na kudade

Shugaban hafsun sojojin kasan Najeriya ya mutu bayan watanni 4 a ofis

Watannin da suka gabata mun kawo muku rahoton cewa, shugaban hafsun sojojin kasa na Najeriya, Laftana Janar Ibrahim Attahiru ya rasu a hatsarin jirgin sama.

Mabanbantan rahotanni sun tabbatar mana da mutuwar babban sojan kasar wanda ya shiga ofis a karshen Junairun 2021.

Jaridar PM News ta bayyana cewa Laftana Janar Ibrahim Attahiru ya mutu a sanadiyyar hatsarin jirgin sama a ranar Juma’a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel