'Ɗan iskan' ajinmu a sakandare ya zama matukin jirgin sama, mu masu kamun kai kuma har yau ba mu da komai

'Ɗan iskan' ajinmu a sakandare ya zama matukin jirgin sama, mu masu kamun kai kuma har yau ba mu da komai

  • Wani ma’abocin amfani da manhajar Twitter, @_deoluwaa ya bayyana yadda wani da su ka yi aji daya dashi a sakandare yana shaye-shaye ya zama matukin jirgin sama
  • A cewar @_deoluwaa, a lokacin babu wanda yake ganin matashin da mutunci amma yanzu ya daukaka, yayin da ya bar su shiryayyun ba su da ko sisi
  • Bayan mutane da dama sun ga wannan wallafar ta shi, sun yi ta cece-kuce inda kowa ya dinga tofa albarkacin bakinsa, hakan ya sa Legit.ng ta wallafa wasu daga cikin tsokacin

Wani matashi wanda ya kira kansa da “talaucinka ya yi yawa da a kai kararka” a kafar sada zumunta, mai amfani da suna @_deoluwaa ya yi wata wallafa a kafar sada zumunta wacce dubannin jama’a su ka dinga tsokaci karkashinta.

Kara karanta wannan

Kabiru Alhasan: Mai hannu daya mai yin sana'ar faskaren itace domin ya rayu a Duniya

A cewarsa, ya na da wani da su ka yi aji daya da shi a sakandare, kuma a lokacin kowa yana yi masa kallon tantirin dan iska.

'Ɗan iskan' ajinmu a sakandare ya zama matukin jirgin sama, mu masu kamun kai kuma har yau ba mu da komai
'Dan iskan ajin mu ya zama matukin jirgi, mu masu kamun kai har yau ba labari. Photo credit: FG Trade, Juanmonino
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda mutumin ya wallafa:

“Dan ajinmu a sakandare wanda ake jan kunnen yara daga bin shi. Yana shaye-shaye tun lokacin da muke aji biyu zuwa na uku a sakandare.”

Abin mamaki, matashin wanda ya ce a yanzu shi ba mai hannu da shuni bane, ya bayyana cewa abokinsa, wanda a baya shine 'dan iskan' aji yanzu ya zama matukin jirgin sama kuma attajiri.

“Abin da zai baka mamaki shine yadda yanzu ya daukaka ya zama matukin jirgin sama a Amurka. Ni kuma wanda na fi kowa hazaka da halaye na gari banda komai."

Tsokacin jama’a

Mutane da dama sun dinga yin tsokaci iri-iri karkashin wallafar.

Kara karanta wannan

Wallafar da Naziru Sarkin waƙa ya yi akan dukan mata ta janyo cece-kuce

DanielRegha ya ce:

“Farkon abinda ya dace iyaye su yi shi ne su koya wa yaransu dabi’u na kwarai kuma abinda iyayenka su ka yi kenan, sun ja kunnenka akan masu shaye-shaye. Batun kuma dauka a rayuwa, ba wani abu bane. Ka daina hada rayuwarka da ta wani saboda baka san abinda su ka yi ba da suka samu wannan daukakar.”

Deoluwa ya ce:

“Ban fahimci abinda mutane su ke daukar arziki ba. Wannan fa abu ne na duniya. Idan ka so ka ba danka kyautar sigari ranar da ya cika shekaru biyar, kai ka sani.”

Bayan rayuwa cikin daji yana cin ciyawa, yanzu wankan sutturu na alfarma ya ke yi, ana girmama shi a gari

A wani rahoton, wani matashi, Nsanzimana Elie ya kasance a baya ya na zama cikin daji saboda yanayin suffar sa, sannan mutanen kauyen sa har tonon sa su ke yi.

Akwai wadanda su ke kiran sa da biri, ashe daukaka ta na nan biye da shi, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Birkin babbar mota ya balle, ta murkushe kananan yara 'yan makaranta

Mahaifiyar Elie ta ce Ubangiji ya amshi addu’ar ta na ba ta shi da ya yi bayan yaran ta 5 duk sun rasu, kuma ba ta kunyar nuna shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel