Yadda muka rarrabe kudin Covid-19: Ga makuden da muka bai wa kowacce jihar, FG

Yadda muka rarrabe kudin Covid-19: Ga makuden da muka bai wa kowacce jihar, FG

  • Jihohin kasar nan biyu ne suka samu sama da miliyan biyu daga gwamnatin tarayya a kokarin dakile radadin annobar korona
  • Kamar yadda kwamitin fadar shugaban kasa na yaki da cutar korona ya bayyana, gwamnatin Legas ta samu N10 biliyan inda Kano ta samu N5 biliyan
  • A yayin karin bayani kan kudaden da jihohi suka samu, kwamitin fadar shugaban kasar ya ce jihohin Ondo, Borno, Ribas da Anambra kowanne ya samu N1 biliyan

FCT, Abuja - 'Yan Najeriyan da basu tabbatar da cewa gwamnatocin jihohi sun samu wani abu daga gwamnatin tarayya ba domin dakile cutar korona, yanzu za su iya kwantar da hankulansu domin kwamitin fadar shugaban kasa ya yi bayani.

Kamar yadda kwamitin fadar shugaban kasan na yaki da cutar korona ya sanar, an rarrabe dukiya tsakanin jihohin kasar nan wurin dakile cutar korona.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi yayin da buhun siminti ya kai N4,600 a Najeriya

Yadda muka rarrabe kudin Covid-19: Ga makuden da muka bai wa kowacce jihar, FG
Yadda muka rarrabe kudin Covid-19: Ga makuden da muka bai wa kowacce jihar, FG. Hoto daga NCDC
Asali: Facebook

Kamar yadda kwamitin Boss Mustapha ya fitar a wata takarda, ya ce jihar Legas ta samu naira biliyan goma yayin da jihar Kano ta samu naira biliyan biyar sai kuma sauran jihohi har da gwamnatin tarayya suka samu naira biliyan daddaya, jaridar Punch ta ruwaito.

Ya ce:

"Tagomashin da aka rarrabe wa jihohi har da babban birnin tarayya su ne kamar haka: Jihar Legas ta samu naira biliyan goma, jihar Kano ta samu naira biliyan biyar inda sauran jihohin tare da birnin tarayya suka samu naira biliyan daddaya kowannensu."

Tallafin COVID-19: Mun raba wa gwamnoni ton 70,000 na kayan abinci - Ministar jin ƙai

A wani labari na daban, ministar jin ƙai, Sadiya Umar Farooq ta bayyana cewa ma’aikatarta ta rabawa gwamnonin jihohi 36 kayan abinci har tan 70,000 a lokacin kullen annobar korona.

Kara karanta wannan

2023: Ta kacame tsakanin gwamnonin APC kan batun fitowa takarar Tinubu

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a zantawarta da sashin Hausa na BBC a ranar Talata a Zamfara, ministar ta ce ta kuma raba tirelolin shinkafa 145 zuwa wadannan jihohi.

"A bangarena na yi aikina. Mun raba kayan abinci zuwa ga gwamnonin jiha kuma ba a tsakar dare bane, kowa ya gani.
“Kimanin tan 70,000 na kayan abinci aka raba. Shinkafar da muka samu daga hukumar kwastam mun raba shi zuwa jihohi 36, wasu kayan hatsi ne kawai aka raba zuwa jihohi 24,” in ji ministar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel