Tallafin COVID-19: Mun raba wa gwamnoni ton 70,000 na kayan abinci - Ministar jin ƙai

Tallafin COVID-19: Mun raba wa gwamnoni ton 70,000 na kayan abinci - Ministar jin ƙai

- Ministar jin ƙai, Sadiya Umar Farooq, ta kaddamar da cewa gwamnatin tarayya ta raba tan 70,000 na kayan abinci ga gwamnonin jiha a matsayin tallafin korona

- Wasu bata gari a fadin kasar sun sace kayan da ke rumbunan ajiyar kayan korona

- Farooq ta ce an bukaci gwamnonin jiha su raba kayayyakin abincin tun daga lokacin da aka mika masu

Ministar jin ƙai, Sadiya Umar Farooq ta bayyana cewa ma’aikatarta ta rabawa gwamnonin jihohi 36 kayan abinci har tan 70,000 a lokacin kullen annobar korona.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a zantawarta da sashin Hausa na BBC a ranar Talata a Zamfara, ministar ta ce ta kuma raba tirelolin shinkafa 145 zuwa wadannan jihohi.

KU KARANTA KUMA: Sun ji uwar bari: Ɓata gari sun fara maido da kayan da suka sata a Adamawa

Tallafin COVID-19: Mun raba wa gwamnoni ton 70,000 na kayan abinci - Ministar jin ƙai
Tallafin COVID-19: Mun raba wa gwamnoni ton 70,000 na kayan abinci - Ministar jin ƙai Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

"A bangarena na yi aikina. Mun raba kayan abinci zuwa ga gwamnonin jiha kuma ba a tsakar dare bane, kowa ya gani.

“Kimanin tan 70,000 na kayan abinci aka raba. Shinkafar da muka samu daga hukumar kwastam mun raba shi zuwa jihohi 36, wasu kayan hatsi ne kawai aka raba zuwa jihohi 24,” in ji ministar.

Kan dalilan da wasu gwamnonin jiha suka bayar na rashin raba kayan abincin, cewa korona za ta dawo a karo na biyu, ministar ta bayyana cewa wannan ya rage gare su.

“Ya rage masu su amsa wannan tambayar, ni dai na raba musu kuma ina da shaidar hakan, gaskiya ta riga ta fito fili,” inji ta.

KU KARANTA KUMA: 2023: Kudu maso gabas ne ya kamata ya samar da magajin Buhari – Gwamna Umahi

Ta kara da cewa ma’aikatar ta umarci gwamnonin su rabawa al’ummar jihohinsu kayan abincin tun a lokacin da aka mika masu lokacin kullen korona, kamar yadda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umurta.

Ta ce gwanati za ta sake duba yuwuwar ba jihohin wasu kayan tallafin kasancewar bata gari sun kwashe wasu daga cikin wadancan da aka basu.

A wani labarin, mazauna Lagas sun roki jami’an yan sanda da su koma bakin aiki sannan su tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin jama’a, jaridar The Nation ta ruwaito.

Sun yi wannan roko ne a ranar Talata, 27 ga watan Oktoba, a kafofin soshiyal midiya sakamakon rashin yan sanda a titunan Lagas.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel