Hankula sun tashi yayin da buhun siminti ya kai N4,600 a Najeriya

Hankula sun tashi yayin da buhun siminti ya kai N4,600 a Najeriya

  • Hauhawar farashin kaya a Najeriya ya janyo kusan komai ya kara tsada a fadin kasar nan har da kayayyakin gini
  • Hatta siminti na gine-gine ba a bar shi a baya ba inda tsadar shi a cikin watanni 6 ya nunka asalin farashin shi
  • Masana tattalin arziki sun ce abin zai ci gaba matsawar gwamnati da masu ruwa da tsaki ba su dakatar da hakan ba

Legas - Jaridar The Guardian ta bayyana yadda farashin kaya suka ninku ciki har da siminti da kayan gine-gine a kasuwannin kasar.

Kamar yadda rahoton ya nuna, karin tsadar kayan gine-gine yana janyo tsadar gidaje sakamakon kudaden da ake narkawa wurin ginasu.

Hankula sun tashi yayin da buhun siminti ya kai N4,600 a Najeriya
Hankula sun tashi yayin da buhun siminti ya kai N4,600 a Najeriya. Hoto daga The Guardian
Asali: UGC

An shawarci gwamnatin Buhari ta yi wani abu wurin dakatar da hauhawar farashin kaya a cikin Najeriya.

Kara karanta wannan

2023: Ta kacame tsakanin gwamnonin APC kan batun fitowa takarar Tinubu

Daga Disamban 2020 zuwa Nuwamban 2021, tsadar siminti ta nunku da kaso 44% wanda hakan ya janyo tsadar bulo da sauran kayan gini.

Cikin watanni 6 da suka gabata, siminti ya tashi daga N3,200 zuwa N4,600 ga kowacce buhu mai nauyin 50kg.

Wani dilan kaya, Mr Sunday Ilesanmi, wanda ya tabbatar da wannan tashin farashin daga kamfani, ya bayyana cewa:

“Tsadar siminti cikin kwanakin nan sai karuwa yake yi. Kuma ya ki sauka. Dama idan lokacin bukukuwa suka karato kudaden kaya suna hauhawa, har da na siminti. Amma kuma duk da tsadar jama’a su na ta siya don ba su da yadda za su yi.”

Yayin tattaunawa da shugaban hukuntar kula da gine-gine da kasuwancinsu, Mr Kayode Ogunji ya ce babbar matsalar da ake fuskanta shine idan masana’antu suka lura ana bukatar wani abu, sai su daga farashi.

Kara karanta wannan

Shugabancin 2023: Za mu durƙusa har ƙasa don nema wa kudu maso gabas goyon bayan sauran yankuna, Ezeife

Sai dai a cewarsa kara tsadar kudin canji na kasashen waje ne ke kara daga farashin siminti.

Ya kara da cewa:

“Akwai ayyukan gine-gine da ake ta yi a jihohi, kasa da kuma gidajen jama’a. Don haka kowa ba shi da yadda zai yi sai ya siya siminti.
“Ba zan yi mamaki ba idan na ga shekarar 2022 ta yi sun kuma kara farashin siminti.”

A baya, shugaban hukumar gine-gine, reshen jihar Legas, Mr Adelaja Adekanmbu ya bukaci a samu inganci da kuma yawan kaya don samun rahusa.

Ya kula da yadda talakawa su ke ta fama yayin da kayan gini kamar rodi da siminti su ke ta tsada a kasuwanni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel