Kungiyar kwadago ta fara shiryawa yadda jama’a za su yaki shirin kai litar man fetur N340

Kungiyar kwadago ta fara shiryawa yadda jama’a za su yaki shirin kai litar man fetur N340

  • Kungiyar ‘yan kwadago ta kasa watau NLC tayi magana a game da shirin kai litar fetur N340 a 2022
  • Shugaban NLC, Kwamred Ayuba Wabba yace ba za su amince a janye tallafin mai haka kurum ba
  • Ayuba Wabba ya zargi gwamnatin tarayya ta biyewa duk abin da kungiyar IMF ta zo mata da shi

Abuja - A ranar Litinin, 6 ga watan Disamba, 2021, kungiyar kwadago ta kasa watau NLC ta bayyana cewa ta fara shirin yakar yunkurin kara kudin fetur.

Vanguard tace NLC za ta jawo mutane domin su yaki shirin da gwamnatin tarayya ta ke yi na kara farashin litar man fetur daga N165 zuwa zuwa N340 a 2022.

Da shugaban kungiyar NLC ta kasa, Kwamred Ayuba Wabba yake magana a wajen wani taro a Ilorin, jihar Kwara, yace ba za su yarda da karin kudin fetur ba.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi yayin da buhun siminti ya kai N4,600 a Najeriya

Kwamred Ayuba Wabba yace za su yaki gwamnatin tarayya a kan kara farashin litar mai ba tare da an kawo tsare-tsaren da za su magance radadin tsadar mai ba.

Za a samu matsala idan ana bin ta IMF - NLC

Ayuba Wabba yace idan gwamnati tayi nasarar kai litar man fetur N320 ko N340, hakan zai yi tasiri wajen jawo tsadar kayan abinci da ma kudin hawa motoci.

Kungiyar kwadago
'Yan kwadago su na zanga-zanga Hoto: www.nairaland.com
Asali: UGC

Kwamred Wabba ya koka da cewa a cikin kasashen da ke cikin kungiyar OPEC, Najeriya kadai ta ke biyewa miyagun shawarwarin da kungiyar IMF ke badawa.

“Maganar cewa gwamnati ta cire hannunta daga harkar fetur, ba abu ba ne da za mu runguma. Mun fadi ba tare da boye-boye ba.” – Ayuba Wabba.

Idan an janye tallafi, farashi zai karu inji Wabba

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Al'amarin ya isa haka, Matasan arewa sun fara yi wa Buhari bore

Ko batun cewa idan an janye tallafin fetur, farashin mai zai rika sauka, Wabba yace ba gaskiya ba ne.

“Lokacin da gangar danyen mai ya zama kusan kyauta a kasuwar Duniya, farashin kananziri da dizil da aka cire masu tallafi ba su taba saukowa ba.”
“Asali ma tashi su ka rika yi a lokacin. ‘Yan kasuwa na gefe su na cin kazamar riba. Abin da zai faru kenan idan Najeriya ta amince da tsarin." - NLC.

Rahoton yace shugaban na NLC ya ba gwamnati shawarwarin da ya kamata ta dauka, yace amma cire tallafi zai jawo karin albashin da aka yi ya zama a banza.

Ba mulkin farar hula ake yi ba

A makon nan aka ji babban Lauyan Najeriya, Kanu Agabi SAN ya bayyana cewa kama-karyar sojoji ta fi wannan tsarin da ake kai a yau da sunan damukaradiyya.

Kanu Agabi yace an yi amfani da tsarin mulki, an ba shugaban kasa da gwamnoni ikon da ya yi yawa, sannan yace ana amfani da wannan iko a murkushe 'yan adawa.

Kara karanta wannan

Litar man fetur zai zarce N340 a farkon shekarar 2022 idan gwamnati ta cire tallafi - ‘Yan kasuwa

Asali: Legit.ng

Online view pixel