Rashin tsaro: Al'amarin ya isa haka, Matasan arewa sun fara yi wa Buhari bore

Rashin tsaro: Al'amarin ya isa haka, Matasan arewa sun fara yi wa Buhari bore

  • Matasan arewacin Najeriya sun yi kira ga shugaba Buhari da ya sauya salon tsaro tare da fatattakar mai bashi shawara kan tsaron kasa, Manjo Janar Babagana Monguno
  • Gamayyar kungiyoyin matasan mai suna NEYGA, ta ce matukar gwamnatin tarayya ba ta dauka mataki ba nan da mako 2, za su fito zanga-zanga a arewacin Najeriya
  • Kungiyar ta ce tura ta kai bango kuma hakan ya isa, asarar rayuka da kadarorin da ake yi a arewacin kasar nan ba zai yuwu a cigaba ba

Matasan arewa sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta sauya salon tsarin tsaro tare da sallamar mai bayar da shawara kan tsaron kasa, Manjo Janar Babagana Monguno kan kashe-kashe da farmakin da ake ta kai wa yankunan arewacin kasar nan.

Kungiyar, wacce ta hada kungiyoyin matasan arewa karkashin uwar kungiya mai suna Northern Ethnic Group Assembly (NEYGA), a wata takarda da ta sa hannu a kai ranar Lahadi ta hannun kakakin ta, Ibrahim Dan-Musa, ta ce wannan kiran ya zama dole sakamakon tsanantar rashin tsaro a arewa, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Jerin kasashe 14 da gwamnatin Saudiyya ta haramtawa shiga kasarta saboda Korona

Rashin tsaro: Al'amarin ya isa haka, Matasan arewa sun fara yi wa Buhari bore
Rashin tsaro: Al'amarin ya isa haka, Matasan arewa sun fara yi wa Buhari bore. Hoto daga Vanguardngr.com
Asali: UGC

Vanguard ta ruwaito cewa, kungiyoyin sun koka kan tsanantar kashe-kashen a yankunan arewacin Najeriya da yadda ya shafi tattalin arzikinta, sun yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya dauka mataki kwakwara wurin dakile yaduwar rashin tsaron.

Kungiyar ta bai wa gwamnatin tarayya wa'adin makonni biyu kan dakile kashe-kashen arewaci inda suka ce idan hakan ba ta faru ba, matasa za su fito kwan su da kwarkwata wurin zanga-zanga.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Abun takaici ne yadda wannan kungiyar ke tunatar da gwamnatin tarayya da sauran gwamnatoci kan hakkin da ke kansu, ballantana ga wadanda aka zaba wurin bai wa rayuka da kadarori kariya.
“A cikin shekaru biyar na mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari, a maimakon rage rashin tsaro, sai abun ya karu inda hakan ya kawo rashin wasu mutane da kadarori ta yadda tarihi ba zai manta da su ba.

Kara karanta wannan

Ka ceto 'yan Najeriya daga yunwa da rashin tsaro, Agbekoya ga Buhari

"A matsayinmu na 'yan kasa nagari, hakkinmu ne mu daga murya tare da kira kan kashe-kashen da ake yi a fadin kasar nan ballantana arewa a kowacce rana.
"Kungiyar na cewa, "ya isa haka" kuma a kawo karshen kashe-kashen nan a kauyukanmu da kuma halin ko in kula da gwamnati ke nuna mana tare da hukumomin ta da ke arewa."

Matasan Najeriya ba su shirya karbar shugabanci ba, Mamban APC

A wani labari na daban, mamba a jam'iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Ribas, Karibi Bob Manuel, ya ca matasan Najeriya ba su da ra'ayin bibiyar shugabanninsu domin karbar shugabanci.

Bob Manuel ya sanar da kamfanin daillancin labaran Najeriya a Fatakwal jihar Ribas a ranar Juma'a cewa, yanayin yadda matasa ke martani kan manyan abubuwan da ke faruwa a kasar nan ne ya nuna hakan, Daily Trust ta ruwaito.

"Muna cikin wani hali wanda matasa suke nuna kamar komai daidai tare da sakarcin bibiyar shugabannin siyasa ba tare da wani tunani ba.

Kara karanta wannan

Yawan 'yan Najeriya na bamu tsoro, dole mu yi wani abu, inji gwamnatin Buhari

"Matasa suna yi kamar wasu wadanda aka siya ko kuma marasa alkibla wadanda a koyaushe ake juya mu son rai tamkar sakako kuma ake nuna mana abinda ya dace mu yi," ya jajanta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel