Samma-kal: Da mulkin farar hular nan, gara gwamnatin Sojoji inji Ministan Obasanjo

Samma-kal: Da mulkin farar hular nan, gara gwamnatin Sojoji inji Ministan Obasanjo

  • Kanu Godwin Agabi ya soki tsarin mulkin da ake amfani da shi, yace bai da maraba da mulkin soja
  • Babban lauyan ya bayyana wannan ne a wajen wata lacca da ya gabatar a Garin Yenagoa, Bayelsa
  • Agabi SAN yace ana amfani da kundin tsarin mulki ana gwamnatin kama-karya a harkar siyasa

Bayelsa - Tsohon babban Ministan shari’a na kasa, Kanu Godwin Agabi ya yi kaca-kaca da tsarin da Najeriya take tafiya a kai da sunan mulkin farar hula.

Jaridar This Day ta rahoto Kanu Godwin Agabi SAN yana cewa tsarin damukaradiyyan da kasar nan ta ke aiki da shi ya ba shugaban kasa karfi da yawa.

Tsohon lauyan na gwamnatin tarayyar ya bayyana haka ne da yake bayani a wajen wata lacca da aka shirya domin tunawa da Mai shari'a Ambros Allagoa.

Kara karanta wannan

Zama na a gidan yari yasa na gane duniya babu tabbas, Sanata Kalu ya bayyana darussan da ya koya

Rahoton yace Marigayi mai shari’a, Ambros Allagoa shi ne mutumin Najeriya na farko da ya rike kujerar babban Alkalin Alkalai a tarihin tsohuwar jihar Ribas.

An tuna da Ambros Allagoa

Da yake bayani a wajen taron a garin Yenagoa, jihar Bayelsa, Agabi yace mulkin sojoji ake yi da sunan farar hula, yace an fake ne kurum da tsarin mulki.

Ministan Obasanjo
Kanu Agabi SAN Hoto: Facebook
Asali: Facebook

Allah wadaran wannan siyasa

“Tsarin gwamnatin da ake yi kama-karya ne kurum aka fake da tsarin mulki, saboda an tattara karfin an ba mutum daya; shugaban kasa ne ko gwamna.”
“Mun zabi wannan tsari saboda akwai yiwuwar samun rabuwar kai a kasa, da sa ran cewa idan iko ya fada kan mutum daya, za a gina kasa.” – Agabi SAN.

Babban Lauyan ya kara da cewa siyasar da ake yi a kasar nan ita ce a kassara ‘yan adawa.

Kara karanta wannan

Shekara 1 da janye dogon yajin-aiki, akwai yiwuwar a sake rufe jami’o’i gwamnati a Najeriya

A wajen wannan lacca, Agabi ya ce dole gwamnatoci a kowane mataki su fahimci cewa adawa mai ma’ana ta na da amfani domin a bunkasa siyasar kasar.

“Muddin aka kashe adawa ko ba ta aiki, gwamnati ba za tayi aiki da kyau ba, kuma idan aka samu wannan, bangaren shari’a ba zai yi aiki da kyau ba.”

EFCC vs Fayose

A makon da ya gabata ne ku ka ji cewa lauyoyin Hukumar EFCC sun kawo shaidu sama da 10 shari’arsu da tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Peter Fayose.

EFCC na zargin Ayodele Fayose da laifuffuka da-dama tun da ya sauka daga kujerar gwamna. Daga ciki akwai laifin karbar kudi daga hannun Musliu Obanikoro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel