Da duminsa: Ma'aikatan Npower sun fito zanga-zanga a Abuja kan rashin biyansu alawus

Da duminsa: Ma'aikatan Npower sun fito zanga-zanga a Abuja kan rashin biyansu alawus

  • Ma'aikatan hukumar Npower sun balle da zanga-zanga a safiyar Litinin a gaban ofishin hukumar aikin gwamnati da ke Kubwa, Abuja
  • Kamar yadda fusatattun ma'aikatan suka sanar, an rike musu albashinsu na watanni uku kuma suna fama da yunwa da ciwuka
  • Wani jami'in hukumar wanda ya fito tare da yin jawabi ga ma'aikata, ya ce a mako mai zuwa za su sakarwa ma'aikatan kudadensu

Kubwa, Abuja - Wasu ma'aikatan Npower a safiyar Litinin sun fito zanga-zangar lumana inda suka mamaye hukumar ayyukan gwamnati da ke Kubwa, a cikin babban birnin tarayyar kan rashin biyansu alawus din su.

Masu zanga-zangar lumanan suna bukatar a biya su kudaden alawus din su na watanni uku wanda hukumar ta rike, SaharaReporters ta ruwaito.

Da duminsa: Ma'aikatan Npower sun fito zanga-zanga a Abuja kan rashin biyansu alawus
Da duminsa: Ma'aikatan Npower sun fito zanga-zanga a Abuja kan rashin biyansu alawus
Asali: Original

SaharaReporters ta ruwaito cewa, kowanne ma'aikacin ana biyansa kudi har N42,000 na cin abinci tare da N10,000 a kowanne wata.

Kamar yadda daya daga cikin masu zanga-zangar, Michael Bright, wanda ya zanta da SaharaReporters yace, har yanzu ba a biya su kudin abinci ba na watan Disamba, lamarin da yace ya bar wasu cikin yunwa da jinya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce, "An mayar da mu tamkar bayi a nan. Kamar gwamnati ta kwaso mu daga jihohinmu ta kawo mu nan Abuja ne domin ta kashe mu da yunwa.
"Muna ta jure yunwa tunda muka zo nan. Ba za mu iya jurewa ba, hakan yasa muka fito zanga-zanga a yau. Dole ne a gaggauta yi mana wani abu."

SaharaReporters ta gano cewa, ayyukan hukumar sun gurgunce a ranar Litinin saboda zanga-zangar da fusatattun ma'aikatan suka fito.

Duk da wani jami'in hukumar wanda ya fito daga bisani yayi jawabi ga fusatattun masu zanga-zangar, ya ce za a biya su alawus din su zuwa karshen makon nan.

Hukumar Npower na karkashin kulawar ma'aikatar walwalwa da jin kan 'yan kasa karkashin shugabancin minista Sadiya Umar Farouk.

Gwamnatin Buhari ta fara kaddamar da shirin N-Power a karo na uku

A wani labari na daban, Gwamnatin tarayya a ranar Litinin 23 ga watan Agustan 2021 ta fara kaddamar da shirin N-Power rukunin C shashi na farko, The Nation ta ruwaito.

Ma'aikatar agaji da ayyukan jin kai ta kasa ta fara aikin yin rajista na rukuni na uku na masu cin gajiyar shirin a ranar 26 ga Yuni, 2020.

Ministar agaji da ayyukan jin kai, Sadiya Farouq ta ce sama da mutum miliyan shida suka nuna sha'awarsu ga cin gajiyar shirin.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel