Da duminsa: Kotun daukaka kara ta sako faston da aka yanke wa hukuncin daurin rai da rai

Da duminsa: Kotun daukaka kara ta sako faston da aka yanke wa hukuncin daurin rai da rai

  • Kotun daukaka a garin Akure da ke jihar Ondo ta sako shugaban cocin Sotitobire, Prophet Babatunde Alfa
  • Da farko wata babbar kotun tarayya da ke zama a Ondo ta yanke wa faston hukuncin daurin rai da rai a gidan yari
  • Wani yaro ne mai watanni 13 ya yi batan dabo a cocin bayan iyayensa sun je da shi bauta, lamarin da yasa aka kone cocin

Kotun daukaka kara da ke zama a Akure, ta sako shugaban cocin Sotitobire Praising Chapel, Prophet Babatunde Alfa, wanda wata babbar kotun jihar Ondo ta yanke wa daurin rai da rai.

Prophet Alfa wanda aka daure a shekarar da ta gabata kan batan dabon da yawo mai shekara daya da wata daya, Gold Kolawole yayi a cocinsa, ya samu 'yancinsa, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sabbin hotunan El-Rufai inda ya ɗau wankan jins tamkar wani saurayi yayin da ya fita duba wasu ayyukan jiharsa

Da duminsa: Kotun daukaka kara ta sako faston da aka yanke wa hukuncin daurin rai da rai
Da duminsa: Kotun daukaka kara ta sako faston da aka yanke wa hukuncin daurin rai da rai
Asali: Original

Gold, wanda har a yau ba a gan shi ba, an je da shi cocin ne amma har yanzu shiru kake ji, babu amo balle labarinsa.

The Nation ta ruwaito cewa, sai dai, fusatattun jama'a sun bankawa cocin Alfa wuta inda ta kurmushe kurmus.

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel