Zama na a gidan yari yasa na gane duniya babu tabbas, Sanata Kalu ya bayyana darussan da ya koya

Zama na a gidan yari yasa na gane duniya babu tabbas, Sanata Kalu ya bayyana darussan da ya koya

  • Bulaliyar majalisar dattawa, Orji Uzor Kalu a Abuja a ranar Lahadi ya wallafa murnar cika shekaru biyu bayan fitowarsa gidan yari
  • Hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC, ta zargesa da waddaka da N7.1 biliyan na jihar Abia kuma an daure shi a 2019
  • Kamar yadda dan majalisar ya bayyana, ya ce an garkame shi na tsawon watanni shida a kan laifin da bai yi ba amma ya fawwalawa Ubangiji lamurransa

Abuja - Tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu a ranar Lahadi, 5 ga watan Disamba, ya yi murnar cika shekaru biyu da fitowa daga gidan gyaran hali na Kuje da ke Abuja.

A yayin bayyana abinda ya fuskanta a gidan yarin Kuje, Sanata Orji Uzor Kalu ya bayyana cewa rayuwar duka babu tabbas a cikinta.

Kara karanta wannan

A halin yanzu, masu garkuwa da mutane 'yan ta'adda ne, Malami

Zama na a gidan yari yasa na gane duniya babu tabbas, Sanata Kalu ya bayyana darussan da ya koya
Zama na a gidan yari yasa na gane duniya babu tabbas, Sanata Kalu ya bayyana darussan da ya koya. Hoto daga Orji Uzor Kalu
Asali: Facebook

Bulaliyar majalisar dattawan, Uzor Kalu ya je shafinsa na Facebook inda ya bayar da labarin darussan rayuwa da ya koya a gidan yarin.

Dan majalisar ya tuna lokacin da yayi zaman gidan yarin Kuje inda yace watanni shidan da yayi a gidan duk yin Allah ne. Ya kara da cewa, an garkame shi ne kan laifin da bai aikata ba.

Abinda ya wallafa

"Abokai na da 'yan kasa ta, ina godiya ga Ubangiji kan zaman watanni shida a gidan yarin Kuje, Ubangiji ya sani, ba na tsoron kowa fiye da shi. Wadanda suka shirya min zagon kasa sun so batar da ni ne ko ta kowanne hali.
"Amma kamar Yakub na Injila, akwai hikima na yadda Ubangiji ya bar lamarin ya faru da ni na wucin gadi. Yanayin yadda na ke kallon rayuwa ya canza bayan watanni shidan nan.

Kara karanta wannan

A cikin shekaru 3, motoci 30 na sata, Wanda ake zargi da fashi da makami

"Ba wai darussa kadai na koya ba, na canza kuma na zama mutum nagari. Abinda ya faru da ni ya koya min darasi. Na yafe musu saboda ta yuwu ba su san abinda suke yi ba."

An saki Sanata Orji Uzor Kalu daga gidan yari

A wani labari na daban, an saki tsohon gwamnan jihar Abiya kuma Sanata da ci yanzu, Orji Uzor Kalu, daga gidan gyari hali da yammacin Laraba, 3 ga watan Yuni, 2020.

Kakakin hukumar gidajen gyara halin Najeriya NCos, DCC Austin Njoku, wanda ya tabbatar da hakan ya ce an saki Orji kalu ne misalin karfe 5:05 na yamma, Punch ta ruwaito.

Yace: "An saki tsohon gwamna Orji Kalu daga kurkuku karfe 5:05 daidai na yammacin Laraba. An sakeshi ne bayan mun samu takardar umurni da kotu na sakinsa."

Asali: Legit.ng

Online view pixel