Yanzu-yanzu: An saki Sanata Orji Uzor Kalu daga gidan yari
An saki tsohon gwamnan jihar Abiya kuma Sanata da ci yanzu, Orji Uzor Kalu, daga gidan gyari hali da yammacin Laraba, 3 ga watan Yuni, 2020.
Kakakin hukumar gidajen gyara halin Najeriya NCos, DCC Austin Njoku, wanda ya tabbatar da hakan ya ce an saki Orji kalu ne misalin karfe 5:05 na yamma, Punch ta ruwaito.
Yace: "An saki tsohon gwamna Orji Kalu daga kurkuku karfe 5:05 daidai na yammacin Laraba. An sakeshi ne bayan mun samu takardar umurni da kotu na sakinsa."
A ranar Talata, 2 ga watan Yuni, wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a jihar Legas, ta ba da umarnin sakin tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu, daga kurkuku.
A ranar 5 ga watan Dasumba, 2019, aka yankewa Mista Kalu hukuncin daurin na shekaru 12 a gidan dan Kande.
Hakan ya biyo bayan samunsa da laifin yin ruf da ciki a kan N7.1bn tare da kamfaninsa, Slok Nigeria Limited, da kuma wani tsohon Daraktan Kudi a gwamnatin Jihar Abia, Jones Udeogu.
Haka kuma Legit.ng Hausa ta ruwaito cewa, masu zanga-zanga a karkashin kungiyar al'umma masu kishi reshen Abiya ta Arewa, a yau Talata sun mamaye majalisar dokoki ta Tarayya.
Sun yi kira ga shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan da ya yi gaggawar sanya kujerar bulaliyar masu rinjaye a majalisar, Sanata Orji Uzor Kalu a kasuwa.
Mista Kalu ya kasance dan jam’iyya mai ci ta APC kuma har yanzu shi ne Sanata mai wakilcin shiyar Abia ta Arewa a zauren majalisar dattawa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng