A halin yanzu, masu garkuwa da mutane 'yan ta'adda ne, Malami

A halin yanzu, masu garkuwa da mutane 'yan ta'adda ne, Malami

  • Abubakar Malami, SAN, ya tabbatar da cewa masu garkuwa da mutane a halin yanzu a kasar nan 'yan ta'adda ne
  • Kamar yadda ministan ya bayyana, hukuncin babbar kotun tarayyan duk an mika shi ga hukumomin tsaro domin su kiyaye
  • Antoni janar na tarayyan, ya ce duk wanda ya tare wani ya sace shi da karfi da yaji ko kuma yayi amfani da makami, tabbas hukuncin ta'addanci za a yi masa

Ministan shari'a kuma antoni janar na tarayya, Abubakar Malami, ya ce masu garkuwa da mutane a yanzu an ayyana su a matsayin 'yan ta'adda.

Ya ce za a wallafa ayyanawar da kotu ta yi kuma ya bayyana cewa an sanar da dukkan hukumomin tsaro na kasar nan.

Malami ya sanar da hakan ne yayin da ya bayyana a shirin siyasar yau, wani shiri na gidan talabijin na Channels a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Ka ceto 'yan Najeriya daga yunwa da rashin tsaro, Agbekoya ga Buhari

A halin yanzu, masu garkuwa da mutane 'yan ta'adda ne, Malami
A halin yanzu, masu garkuwa da mutane 'yan ta'adda ne, Malami. Hoto daga channelstv.com
Asali: UGC

A ranar Alhamis da ta gabata, wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ayyana 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda. A hukuncin Mai shari'a Taiwo Taiwo, ya bayyana kungiyoyin 'yan bindiga a matsayin kugiyoyin ta'addanci.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wannan hukuncin ya biyo bayan korafin da daraktan gurfanarwa na tarayya, Mohammed Abubakar ya shigar, Punch ta ruwaito.

DPPF ya sanar da kotun cewa, wannan korafin da ya shigar ya mika shi ne domin biyayya ga umarnin shugaban kasa.

A ranar Laraba, Malami ya ce, "Idan ka yi garkuwa da mutum ta hanyar amfani da karfi, ko kuma makamai, toh ka zama dan ta'adda kamar yadda hukuncin kotun ya bayyana. Za ka shiga cikin wadanda za a hukunta ta hanyar amfani da dokokin ta'addanci."

Mun shirya tsaf domin mitsike su: Martanin FG kan ayyana 'yan bindiga matsayin 'yan ta'adda

Kara karanta wannan

Buhari ya tabbatarwa 'yan Najeriya zaman makoki a kasar na daf da zuwa karshe

A wani labari na daban, Antoni janar na tarayya kuma ministan shari'a, Abubakar Malami, SAN, ya ce gwamnatin tarayya ta shirya tsaf domin mitsike 'yan bindiga saboda kotu ta ayyana su a matsayin 'yan ta'adda wanda ofishinsa ya mika da bukatar gaban kotun.

Dr. Umar Jibrilu Gwandu, mai bada shawara na musamman a ofishin antoni janar din ya sanar da hakan ta wata takarda da ya fitar ga manema labarai, Daily Trust ta ruwaito.

Kamar yadda takardar tace, ayyana 'yan bindiga matsayin 'yan ta'adda alamu ne na shirin ofishin antoni janar na tarayya da kuma gwamnatin tarayya na ganin bayansu amma cike da bin doka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel