Ayyana ƴan bindiga ƴan ta'adda ɓata lokaci ne, tunda ba a san su ba, Buba Galadima

Ayyana ƴan bindiga ƴan ta'adda ɓata lokaci ne, tunda ba a san su ba, Buba Galadima

  • Injiniya Buba Galadima, tsohon na hannun daman Shugaba Muhammadu Buhari ya soki ayyana 'yan bindiga yan ta'adda da gwamnati ta yi
  • Galadima ya ce ayyana yan bindiga yan ta'adda ba komai bane illa bata lokaci domin ba a san ko su wanene yan bindigan ba ko inda za a same su
  • A cewarsa, abinda ya kamata gwamnati ta yi shine zartar da hukunci mai tsauri kan duk wanda aka kama yana aikata aiki na ta'addanci a maimakon ayyanawar

Tsohon na hannun daman Shugaba Muhammadu Buhari, Buba Galadima, ya yi watsi da ayyana 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda da Gwamnatin Tarayya ta yi, yana mai cewa bata lokaci ne.

Mai Shari'a Taiwo Taiwo na Kotun Tarayya a Abuja cikin makon da ta gabata ta ayyana ayyukan kungiyoyin 'yan bindiga da 'yan ta'adda a matsayin ta'addanci.

Kara karanta wannan

A halin yanzu, masu garkuwa da mutane 'yan ta'adda ne, Malami

Ayyana ƴan bindiga ƴan ta'adda ɓata lokaci ne, ba a san fuskokinsu, Buba Galadima
Buba Galadima ya ce ayyana 'yan bindiga 'yan ta'adda da gwamnati ta yi bata lokaci ne. Hoto: NewsWireNGR
Asali: Facebook

Da ya ke tsokaci a kan wannan matakin, Galadima, cikin hirar da Vanguard ta yi da shi ya ce:

"Maganan gaskiya, kai baka tunanin bata lokaci ne? Akwai abubuwan da za su biyo baya. Wadanda suka ayyana 'yan bindigan 'yan ta'adda na nufin sun san su amma ba su yi komai a kansu ba. A gani na, bata lokaci ne da jahilci a bangaren wadanda suka yi hakan don ban san su wanene yan bindiga ba ko adireshinsu ta yadda idan sun kai hari ka san inda za ka tafi ka kama su."

Ya cigaba da cewa:

"Abin masu doka a kasar ya dace su yi shine su yi doka mai cewa duk wanda aka kama yana ta'addanci za a kashe shi. Amma ba za ka iya ayyana wani dan ta'adda ba idan baka san adireshinsa ba, ko sunansa. Kawai laifin da suke yi za ka magance.

Kara karanta wannan

Ana wata: Shehin malami ya magantu, ya ce mata su daina yiwa mazajensu girki da aikin gida

"Idan ka kama mutum yana aikata laifin, ka hukunta shi, amma ba wai ka haramta mutanen da ba ka san su ba. Idan ka ayyana 'yan bindiga 'yan ta'adda, kana nufin cewa tuntuni ka san su kenan, kana karya alhalin kuna aiki tare."

Da aka tunatar da shi kan cewa Gumi ya sha gana wa da yan bindigan kuma yana neman a musu afuwa, Galadima ya ce:

"Kana nufin akwai wadanda ba su san IPOB ba? Wadanda suka tafi wurin shugaban kasa suna neman a saki Nnamdi Kanu ba, wanda kowa ya san shine shugaban IPOB? Me yasa ba a kama su ba idan kana cewa a kama Gumi?"

Bana kwatanta IPOB da 'Yan bindiga, Galadima

Galadima ya cigaba da cewa ba yana kwatanta IPOB da yan bindiga bane, duba da cewa IPOB sananen kungiya ce mai lambar asusun ajiyar banki har wasu suna biyan kudi daga kasar waje da gida don ayyukan kungiyar.

Kara karanta wannan

Buhari ya tabbatarwa 'yan Najeriya zaman makoki a kasar na daf da zuwa karshe

"Shin ko akwai lambar asusun banki na yan bindiga," Ya tambaya.

Don haka ba kwatanta su na ke yi ba domin daya sananniyar kungiya ce yayin da dayan kuma ba a san su ba amma wasu ayyukansu daya ne.

Buhari ga jami'an tsaro: Bana son sake jin motsin ƴan bindigan hanyar Kaduna zuwa Abuja

A wani labarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci shugabannin tsaron kasar nan da su kawo karshen ta’addancin da ke aukuwa a kasa musamman a hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ya sanar da hakan a ranar Alhamis bayan wani taro da shugaban kasa ya yi da kwamitin tsaron kasa, NSC a fadarsa da ke Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

A cewarsa shugaban kasan ya ba ‘yan sanda da duk wasu jami’an tsaro ciki har da jami’an binciken sirri umarnin kada su zauna har sai sun kawo karshen ta’addanci, rashin tsaro, amsar kudaden fansa da sauransu a Najeriya.

Kara karanta wannan

Ba zamu hukunta tubabbun yan Boko Haram ba, Farfesa Zulum

Asali: Legit.ng

Online view pixel