Ba fa zamu yarda Musulmi da Musulmi su yi takara a zaben 2023 ba, Cocin PFN

Ba fa zamu yarda Musulmi da Musulmi su yi takara a zaben 2023 ba, Cocin PFN

  • Kungiyar PFN ba zata amince Musulmi ya zama shugaban kasa kuma Musulmi ya zama mataimaki ba
  • Wannan ya biyo bayan kirar da kungiyar MURIC ta Musulmai tayi na cewa mabiyi addinin Islama kuma bayarbe za'a ba mulki a 2023
  • Muhawara na cigaba da gudana tsakanin mabiya addinai biyu yayinda ake tunkarar zaben 2023

Legas - Kungiyar mabiya cocin Pentecostal a Najeriya PFN ta bayyana cewa ta bankado shirin da wasu ke yi baiwa Musulmi biyu tikicin takara kujera shugaba da mataimaki a zaben 2023.

Shugaban PFN, Bishop Wale Oke, ya bayyana hakan a taron gangamin Zee World Congress da ya gudana a Jami'ar Ibadan ranar Litinin, rahoton Sun.

Oke ya bayyana cewa duk da kungiyar ba ta zabi wanda zata marawa baya ba, duk jam'iyyar da ke shirin mayar Kiristoci saniyar ware ba zatayi nasara ba.

Kara karanta wannan

Waiwaye a 2021: Haziƙan Ɗaliban Najeriya 4 Da Suka Karya Tarihin Da Ba a Taɓa Zaton Wani Zai Iya Ba

Yace:

"Da bacin rai wasu yan siyasa na kokarin tayar da tarzoma a kasar nan ta hanyar baiwa Musulmi da Musulmi damar takara a zaben 2023."
"Najeriya fa kasar Kiristoci da Musulmai ne.. Saboda haka ba zamu yarda da tikitin Musulmi da Musulmi ba; ba zamu yarda a ware Kiristoci ba."
"Abinda muke so shine a bi sahun abinda akayi lokacin gwamnatin Obasanjo, Umar Yar'adua da Buhari."
"Duk wanda ke kokarin baiwa Musulmi da Musulmi tikiti shaidanin mutum ne kuma dan wuta. Kuma sai Allah ya ruguza shaidancinsy. Duk jam'iyyar da ta baiwa Musulmi da Musulmi tikiti ata sha kasa. zata ruguje."

Cocin PFN
Ba fa zamu yarda Musulmi da Musulmi su yi takara a zaben 2023 ba, Cocin PFN
Asali: Facebook

Ya zama dole Kirista ya gaji Shugaba Buhari a 2023 idan ana don zaman lafiya, Cocin PFN

Shugaban PFN ya yi kira ga yan Najeriya cewa kasar nan ta kowa ce kuma wajibi ne shugaba Muhammadu Buhari ya bari Kirista ya gajeshi.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari za ta karbo sabon bashi daga bankin muslunci saboda wasu dalilai

A cewarsa, shaidanin mutum ne kawai zai yi kokarin kakaba musu dan takara Musulmi.

Yace:

"Abinda muke so shine Shugaban kasa Kirista. Wajibi ne Buhari ya mika mulki wa Kirista. Kowa ya sani cewa duk wani sabanin haka ba zamu yarda ba. Mambobin cocin PFN milyan 65 ba zasu amince ba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel