Gwamnatin Buhari za ta karbo sabon bashi daga bankin muslunci saboda wasu dalilai

Gwamnatin Buhari za ta karbo sabon bashi daga bankin muslunci saboda wasu dalilai

  • Gwamnatin tarayya ta tuntubi bankin Musulunci don neman taimako kan yadda za a yi ayyukan ilimi a kasar
  • Bayan shafe watanni ana jira, hukumar gudanarwar bankin Musulunci ta amince da bada lamunin da za a biya ba tare da ruwa ba
  • Jihohi tara ne za su ci gajiyar wannan lamuni kuma hukumar kula da ilimin bai daya (UBEC) ce za ta yi aikin kulawa da lamarin

Abuja - Kwamitin gudanarwa na bankin ci gaban Musulunci (IsDB) ya amince da bayar da lamuni na dala miliyan 98 (N40.54bn) domin tallafawa ilimin harsuna a Najeriya.

Lamunin zai taimaka wa yara daga Adamawa, Borno, Gombe, Kaduna, Kano, Kwara, Nasarawa, Neja, da Osun wajen samun cikakken horon harshen Larabci da Turanci.

David Apeh, shugaban hulda da jama'a da yarjejeniya a hukumar kula da ilimin bai daya (UBEC), shine ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka buga a Abuja ranar Laraba 15 ga watan Disamba 2021.

Kara karanta wannan

Dubun yan bindigan da suka kashe mutane a masallaci a jihar Neja ya cika

Cin bashin bankunan muslunci
Gwamnatin Buhari ta koma neman bashi daga bankunan muslunci saboda tsaro | Hoto: Brothers91
Asali: Depositphotos

Tallafin, Apeh ya kuma ce zai taimaka wajen inganta yanayin zamantakewa da tattalin arzikin Najeriya, da samar da ilimi mai inganci, in ji jaridar Sun.

Sauran muhimman abubuwan da suka shafi rancen, a cewar Apeh, shine habaka damar samun ilimi daga tushe, habaka ingancinsa, da kuma karfafa ikon gudanarwar makarantu.

Sakataren zartarwa ya magantu

Taron ya gudana ne karkashin jagorancin Babban Sakataren UBEC, Dakta Hamid Bobboyi, wanda Mataimakin Babban Sakatare (Technical), Farfesa Bala Zakari ya wakilta.

Hakazalika, ya samu halartar wakilan hukumar ta UBEC da kuma wakilan Ma'aikatun Ilimi na Tarayya, Kudi da IsDB.

Bobboyi a nasa jawabin ya sanar da gwamnatocin jihohin cewa aikin rance ne da ya zama dole a biya shi, don haka akwai bukatar tabbatar da aiwatar da shi yadda ya kamata da kuma gudanar da shi cikin tsanaki.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kasafin kudin shekarar 2022 ya samu gagarumin koma baya a Majalisa

Jihohin sun bayyana aniyarsu ta daukar nauyin ayyukan bayan an kammala su yayin da ake sa ran mahalarta taron za su yi wa gwamnonin jihohinsu bayani.

Tribune ta rahoto cewa, kakakin na UBEC ya bayyana cewa tuni hukumar kula da ayyukan ta kasa ta dauki masu gudanar da aikin.

Ya kuma kara da cewa an sayo kayayyakin ofis da kayan aiki ga jihohin tara da suka halarci taron, ya kara da cewa an fara aikin ginin.

Mun fara tattaunawa da bankin duniya domin ciwo sabon bashin gida masarrafan rigakafi, Shugaba Buhari

A wani labarin, shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta fara tattaunawa da bankin Duniya kan yadda zata sami rancen dala miliyan $30m.

Jaridar Punch ta ruwaito shugaban yace gwamnatin zata karbo wadannan kudaden ne domin gida ma'aikatar da zata samar da rigakafi a Najeriya.

Buhari ya kara da cewa za'a fara aikin ginama'aikatar sarrafa rigakafin da za'a gina bisa hadin guiwar kamfanin May & Baker Nigeria Plc shekara mai zuwa.

Kara karanta wannan

Labari mai dadi: Shugaba Buhari ya kara wani kaso mai tsoka a albashin 'yan sanda

Asali: Legit.ng

Online view pixel