'Karin bayani: Gwamnatin Kano tare da yan sanda sun rufe lauyan da ya wakilci bangaren Shekarau a ofishinsa

'Karin bayani: Gwamnatin Kano tare da yan sanda sun rufe lauyan da ya wakilci bangaren Shekarau a ofishinsa

  • Jami'an ma'aikatar filaye tare da jami'an yan sanda a Kano sun rufe ofishin lauyan da ya wakilci bangaren Shekarau a shari'ar shugabancin APC
  • Nureini Jimoh, SAN, ya tabbatar da rufe ofishinsa da aka yi yana mai cewa shi da wasu ma'aikatansa suna ciki yayin da aka garkame kofar ofishin
  • A ranar Talata ne wata kotu da ke Abuja ta rushe zaben da bangaren Gwamna Ganduje ta yi ta tabbatar da hallarcin zaben bangaren Sanata Shekarau

Jihar Kano - Jami'an ma'aikatar filaye tare da yan sanda sun rufe ofishin Lauya Nureini Jimoh, SAN, da ke 16c Murtala Mohammed Way a Kano, Daily Nigerian ta ruwaito.

Mr Jimoh, a ranar Talata shine ya wakilci bangaren Sanata Ibrahim Shekarau inda suka yi nasara kan bangaren Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a rikicin shugabancin jam'iyyar APC a Kano.

Kara karanta wannan

Yan bindiga da Sojojin sun yi musayar wuta a Imo kan umarnin zama a gida na IPOB

Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Kano da Yan sanda sun garkame lauyan da ya wakilci bangaren Shekarau
Gwamnatin Kano tare da 'yan sanda sun rufe lauyan da ya wakilci bangaren Shekarau a ofishinsa. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Lauyan ya tabbatar wa Daily Nigerian da cewa an rufe ofishinsa yayin da shi da sauran ma'aikatansa suke ciki.

Ya ce:

"A halin yanzu da na ke muku magana, ina cikin ginin tare da wasu mutane da dama. Don haka ba mu san ta yadda za mu fita ba."

Daga bisani an turo jami'ai sun bude ofishin

Amma bayan awanni da rufe ofishin, jami'an gwamnatin sun bude su biyu bayan rahotanni da suka ba zu a kafafen watsa labarai game da afkuwar lamarin.

A yayin da wakilin Daily Nigerian ya ziyarci wurin, ya gano cewa Mrs Braji ta umurci jami'an da suke rufe wurin tunda farko su tafi su bude.

Jami'an, da suka taho cikin mota kirar Hilux fara mai lamba KIRS 62, dauke da shugaban tawagarsu, Hassan Idris, sun yi gaggawa sun cire babban kwadon da suka rufe kofar shiga harabar.

Kara karanta wannan

NDLEA: Matar da aka cafke ta hadiyi ledoji 80 na Koken, ta yi kashin su a filin jirgi

Da manema labarai suka tambayi dalilin da yasa aka bude wurin, ya ce:

"Sakataren dindindin ne ya bada umurnin a bude wurin."

Mai magana da yawun yan sandan jihar, DSP Abdullahi Kiyawa ya ziyarci wurin domin bincikar ikirarin da aka yi na cewa akwai hannun yan sanda a lamarin.

Martanin Gwamnatin Jihar Kano kan rushe zaben bangaren Ganduje

A baya, kun ji cewa Antonji Janar kuma kwamishinan Shari'a na jihar Kano, Musa Lawan, ya ce za su daukaka kara bisa hukuncin da kotun tarayyar ta yanke, rahoton Premium Times.

Mr Lawan ya ce gwamnatin tana nazarin hukuncin kafin ta dauki matakin ta na gaba.

Ya ce:

"Muna nazari kan hukuncin domin mu gani ko kotun tana da ikon sauraron karar tunda farko."

Asali: Legit.ng

Online view pixel