Rikicin APC a Kano: Ganduje ya yi martani kan hukuncin kotu na rushe zaɓen ɓangarensa

Rikicin APC a Kano: Ganduje ya yi martani kan hukuncin kotu na rushe zaɓen ɓangarensa

  • Gwamnatin Jihar Kano ta yi martani kan hukuncin kotun tarayya da ta rushe zaben shugabannin APC na bangaren Ganduje
  • Kotun ta jadadda cewa shugabannin da aka zaba na bangaren Sanata Shekarau ne halattattu sannan ta dakatar da tsagin Ganduje da nada sabbin shugabanni
  • Antoni Janar kuma kwamishinan Shari'a na Jihar Kano, Musa Lawan, ya ce suna nazari kuma za su daukaka kara game da hukuncin

Kano - Babban kotu da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta rushe zaben shugabannin jam'iyyar APC na bangaren Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, Premium Times ta ruwaito.

Bangarorin biyu sun yi zabuka biyu a ranar 18 ga watan Oktoba amma uwar jam'iyyar ta amince da zaben da bangaren Gwamna Abdullahi Ganduje ta yi.

Rikicin APC a Kano: Ganduje ya yi martani kan hukuncin kotu na rushe zaɓen ɓangarensa
Gwamna Abdullahi Ganduje zai daukaka kara kan hukuncin kotu na rushe zaben bangarensa na APC a Kano. Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

Bangaren Sanata Ibrahim Shekarau sun zabi Haruna Dan Zago a matsayin shugaban su yayin da bangaren Ganduje suka zabi Abdullahi Abbas.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Kotu ta yanke hukunci kan zaɓen shugabannin APC na tsagin Ganduje da Shekarau a Kano

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daga bisani bayan kafa kwamitin sauraron korafi zai ta tabbatar da Mr Abbas a matsayin halastaccen shugaban jam'iyyar a jihar.

Bangaren Shekarau sun shigar da kara a kotu

Ganin cewa ba su gamsu da matakin da jam'iyyar ta kasa ta yanke ba, bangaren tsohon gwamnan jihar, Sanata Shekarau sun shigar da kara a kotu, suna neman a rushe zaben Ganduje a tabbatar da nasu.

A hukuncinsa, Alkalin kotun, Hamza Mu'azu ya amince da bukatar da bangaren Shekarau suka shigar ya kuma rushe zaben bangaren Ganduje.

Kotun ta kuma hana bangaren na Ganduje sake nada sabbin shugabanni.

Martanin Gwamnatin Jihar Kano

Antonji Janar kuma kwamishinan Shari'a na jihar Kano, Musa Lawan, ya ce za su daukaka kara bisa hukuncin da kotun tarayyar ta yanke, rahoton Premium Times.

Mr Lawan ya ce gwamnatin tana nazarin hukuncin kafin ta dauki matakin ta na gaba.

Kara karanta wannan

Masarautar Dansadau ta yi zaman sulhu da kasurgumin dan bindiga, Ali Kachalla

Ya ce:

"Muna nazari kan hukuncin domin mu gani ko kotun tana da ikon sauraron karar tunda farko."

Kotu ta yanke hukunci kan zaɓen shugabannin APC na tsagin Ganduje da Shekarau a Kano

Tunda farko, kun ji cewa babban kotu mai zamanta a Abuja karkashin Mai Shari'a Hamza Mua'zu ta soke dukkan shugabannin jam'iyyar All Nigeria Peoples Congress da ke biyayya ga Gwamna Abdullahi Ganduje.

Da ya ke yanke hukuncin a ranar Talata, alkalin ya amince ce bangaren Sanata Ibrahim Shekarau ne halatattun zababun shugabanni, Daily Nigerian ta ruwaito.

Wadanda suka shigar da karar sune Muntaka Bala Sulyman da mambobin jam'iyyar su 17,980 yayin da wadanda aka yi kararsu kuma sun hada da APC, Mai Mala Buni, Shugaban Riko, John Akpanudoedehe, da hukumar INEC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel