Shugaba Buhari ya karrama wasu 'yan Najeriya 3 'masu gaskiya'

Shugaba Buhari ya karrama wasu 'yan Najeriya 3 'masu gaskiya'

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Talata, a Abuja, ya karrama wasu ma'aikatan gwamnati biyu, Muhammad Ahmad da Nelson Okoronkwo da wani dalibin Najeriya da ke Japan saboda nuna halin gaskiya da rikon amana.

Hadimin Shugaban Kasa, Femi Adesina ne ya sanar da hakan cikin wata wallafa da ya yi a shafinsa na Facebook.

Shugaba Buhari ya karrama wasu 'yan Najeriya 3 'masu gaskiya'
Shugaba Muhammadu Buhari ya karrama wasu 'yan Najeriya uku masu gaskiya da rikon amana. Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

1. Muhammad Ahmad

Mr Ahmad, mataimakin kwamanda ne hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA.

A baya bayan nan ya gano wani mai safarar miyagun kwayoyi sannan ya sanar da cewa ya bashi cin hancin dallar Amurka 24,500.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Mun gano jarirai da suke karɓar albashi a Borno, Gwamna Zulum

Ya bashi kudin ne a matsayin cin hanci game da binciken da aka yi kan wani hodar iblis ta kilo 28 da ya kai biliyoyin naira.

2. Mr Okoronkwo

Mr Okonronkwo ma'aikaci ne a ma'aikatar tarayya ta sadarwa da al'adu, shima an karrama shi saboda nuna gaskiyarsa da rikon amana a ma'aikatu da dama da ya yi aiki a baya.

A matsayinsa na kwamitin hana daukan ma'aikata ba bisa ka'ida ba, mataimakin direktan ya jagoranci aikin gona ma'aikatan bogi 3000 da korarsu daga aiki.

Ta hakan, ya taimaki gwamnatin tarayya ta adana biliyoyin naira da ake biyan ma'aikatan bogin albashi da alawus.

3. Ikenna Nweke

Mr Ikenne Nweke, dalibi ne mai karatun digirin digir-gir a kasar Japan, ya tsinci jakar kudi dauke da makuden kudi da wasu abubuwa masu muhimmanci.

Ya mayar da kudin zuwa ga hannun yan sanda a kasar Japan ya kuma kin karbar tukwicin kashi 10 cikin 100 na kudin da ya mayar da aka bashi.

Kara karanta wannan

Garba Shehu: Buhari ya cancanci jinjina kan yadda ya shawo kan matsalar tsaro

Shugaba Buhari ya taya su murna

Da ya ke magana game da Nweke, wanda ya hallarci taron da hanyar fasahar bidiyo da sauti na intanet, Buhari ya ce:

"Najeriya na alfahari da shi a can kasar Japan da ya ke saboda nuna halin gaskiya da rikon amana da aka san mu da shi inda ya mayarwa yan sanda jakar kudi.
"Ya kuma ki karbar kashi 10 cikin 100 da aka bashi matsayin tukwici.
"Ni da ICPC mun ayyana shi a matsayin Tauraro na Kungiyar yan kasa masu yaki da rashawa na ICPC.
"Tabbas shi tauraro ne kuma abin koyi ga matasa. Na taya shi murna. Na taya dukkan sauran wadanda aka karrama da satifiket din gaskiya da suka nuna a hukumominsu."

Ana bin kowanne ɗan Najeriya bashin N64,684 bisa basukan da ƙasar ta ci a ƙasashen waje

A wani labarin, kun ji cewa bisa yawan ‘yan Najeriya da kuma yawan basukan da ake bin ta, kowa ya na da N64,684 a kan sa.

Kara karanta wannan

'Kuncin rayuwa ta tunzura ni: Matashin da aka kama da hodar iblisa ta N2.7bn a filin jirgin Abuja

Kamar yadda kowa ya san yawan bashin da Najeriya take ta amsowa daga kasashen ketare, yanzu ko wanne dan Najeriya ya na da bashin $157 ko kuma N64,684 a kan sa.

Bisa wannan kiyasin, masanin tattalin arzikin kasa, Dr. Tayo Bello ya bayyana damuwar sa akai inda ya ce duk da zuzurutun basukan, babu wasu abubuwan ci gaba da aka samar wadanda za su taimaka wurin biyan basukan kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel