Da duminsa: Kamfanin jiragen sama na Emirates za ta dawo da safarar fasinjoji a Najeriya

Da duminsa: Kamfanin jiragen sama na Emirates za ta dawo da safarar fasinjoji a Najeriya

  • Kamfanin jiragen sama na Emirates Airline, ya sanar da cewa zai cigaba da kaiwa da kawowa da fasinjoji daga Najeriya
  • Kamar yadda takardar da kamfanin ya fitar ta nuna, za a cigaba da daukar fasinja daga Najeriya zuwa Dubai a ranar 5 ga Disamba
  • Domin samar da saukakakkiyar hanya ga fasinjoji, jirgin kamfanin zai dinga tashi a kowacce rana

Kamfanin jiragen sama na Daular Larabawa, UAE, Emirates, ya ce zai cigaba da safarar fasinjoji tsakanin Dubai da Najeriya daga ranar 5 ga watan Disamban shekarar nan.

The Nation ta ruwaito cewa, kamfanin jiragen saman ya ce, zai fara karakaina tsakanin Najeriya zuwa Dubai a kowacce rana ta yadda zai samarwa da fasinjoji damar zuwa Dubai.

Da duminsa: Kamfanin jiragen sama na Emirates za ta dawo da safarar fasinjoji a Najeriya
Da duminsa: Kamfanin jiragen sama na Emirates za ta dawo da safarar fasinjoji a Najeriya. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: UGC

Wannan sabon matakin an gano ya biyo bayan sasancin da aka samu tsakaninsu da Najeriya bayan dakatar da su, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sanatoci sun kaure da cacar baki kan rashin adalci a daukar ma'aikata a rundunar soji

A wata takarda, kamfanin jiragen saman ya ce a lokacin annoba, ya kasance mai ankarar da fasinjoji kan duk wani matakin kariya tare da taimakawa yankuna wurin tabbatar da farfadowar tattalin arziki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamfanin jiragen saman ya ce har yanzu ya na aiki tukuru wurin bada bayanai masu amfani ga fasinjoji tare da tabbatar da dakile yaduwar cutar korona ta hanyar binciken fasinjoji ba tare da an taba su ba.

UAE ta haramtawa 'yan Najeriya zuwa Dubai saboda Covid-19

A wani labari na daban, Gwamnatin daular Larabawa (UAE) ta dakatar da shigar da 'yan Najeriya zuwa Dubai a matsayin hanyar dakatar da yaduwar cutar COVID-19.

Wannan umarnin ya biyo bayan sa'o'i 24 da jiragen UAE suka sanar da wannan dakatarwar jirage daga Legas zuwa Abuja.

Babban jirgin da yake kai mutane Dubai daga Najeriya, Air Peace, ya sanar da wannan umarnin na UAE ga fasinjoji. Air Peace ya bayar da hakuri ga fasinjoji akan wannan al'amari, Daily Trust ta wallafa.

Kara karanta wannan

Yan bindiga da Sojojin sun yi musayar wuta a Imo kan umarnin zama a gida na IPOB

"Kamfanin sufurin jiragen sama na Air Peace tana son sanar da mutane cewa gwamnatin UAE ta dakatar da 'yan Najeriya daga shiga UAE a matsayin dokar hana yaduwar COVID-19.
"Duk da dai bata dakatar da mayar da 'yan Najeriya daga Dubai zuwa kasarsu ba. Don haka daukar mutane daga Dubai zuwa Najeriya zai cigaba da wanzuwa har sai 28 ga watan Fabrairun 2021," cewar kamfanin Air Peace.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel