Da duminsa: UAE ta haramtawa 'yan Najeriya zuwa Dubai saboda Covid-19

Da duminsa: UAE ta haramtawa 'yan Najeriya zuwa Dubai saboda Covid-19

- Gwamnatin daular larabawa (UAE) ta dakatar da shigar 'yan Najeriya Dubai ta jiragen sama a matsayin hanyar dakatar da yaduwar COVID-19

- Babban kamfanin jiragen saman Najeriya, Air Peace, wanda yake kai mutane Sharjah-Dubai, ya sanar da fasinjojin da suke Najeriya wannan sakon

- Sai dai bata dakatar da jiragen da suke mayar da 'yan Najeriya kasarsu ba tukunna, don haka dokar bata hau kan juragen da suke dauko mutane daga Dubai zuwa Legas

Gwamnatin daular Larabawa (UAE) ta dakatar da shigar da 'yan Najeriya zuwa Dubai a matsayin hanyar dakatar da yaduwar cutar COVID-19.

Wannan umarnin ya biyo bayan sa'o'i 24 da da jiragen UAE suka sanar da wannan dakatarwar jirage daga Legas zuwa Abuja.

Babban jirgin da yake kai mutane Dubai daga Najeriya, Air Peace, ya sanar da wannan umarnin na UAE ga fasinjoji.

Air Peace ya bayar da hakuri ga fasinjoji akan wannan al'amari, Daily Trust ta wallafa.

KU KARANTA: Bidiyon fusataccen saurayi yana kwace kayan kallo da ya siyawa budurwarsa bayan sun bata

Da duminsa: UAE ta haramtawa 'yan Najeriya zuwa Dubai saboda Covid-19
Da duminsa: UAE ta haramtawa 'yan Najeriya zuwa Dubai saboda Covid-19
Asali: Original

"Kamfanin sufurin jiragen sama na Air Peace tana son sanar da mutane cewa gwamnatin UAE ta dakatar da 'yan Najeriya daga shiga UAE a matsayin dokar hana yaduwar COVID-19.

"Duk da dai bata dakatar da mayar da 'yan Najeriya daga Dubai zuwa kasarsu ba. Don haka daukar mutane daga Dubai zuwa Najeriya zai cigaba da wanzuwa har sai 28 ga watan Fabrairun 2021," cewar kamfanin Air Peace.

Dakatar da zirga-zirgar jirage daga kasa zuwa kasa hanya ce ta dakatar da yaduwar cutar.

Yanzu haka an tabbatar da masu COVID-19 da dama kuma mutane guda miliyan 2.3 ne suka rasa rayukansu.

KU KARANTA: Muna da sabbin dabarun yakar ta'addanci da 'yan bindiga a kasar nan, Osinbajo

A wani labari na daban, wani mai gidan haya mai suna Mufutau Ojomu a ranar Laraba ya bayyana a gaban wata kotun majistare da ke Ogudu a jihar Legas a kan zarginsa da ake da yi wa 'yar haya mugun duka bayan ya bata notis.

'Yan sandan suna zargin Ojomu da laifin hada kai wurin aikata laifi da cin zarafi, Vanguard ta wallafa.

Dan sanda mai gabatar da kara, Dojour Perezi, ya sanar da kotu cewa mai kare kan shi ya aikata laifin a ranar 27 ga watan Disamban 2020 a layin Yisa Omotunde da ke yankin Alapere a jihar Legas.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel