Gwamnan Adamawa ya rabawa Sarakunan gargajiyar jihar manyan Motoci

Gwamnan Adamawa ya rabawa Sarakunan gargajiyar jihar manyan Motoci

  • Gwamnan jihar Adamawa ya bayyana yadda aka fara shirin yakin neman zabensa na shekarar 2023
  • Gwamna Fintiri ya yi sanarwa ranar Laraba cewa Kansilolin jihar sun hada masa N22m don sayan Fam na takara
  • Gwamna Ahmad Umaru Fintiri ya rabawa Sarakunan gargajiya sabbin manyan motoci saboda hadin kan da suke basa

Yola - Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jihar Adamawa ranar Laraba, 1 ga Disamba, ya rabawa manyan Sarakunan gargajiya motocin SUV da Hilux..

Gwamnan wanda ya bayyana hotunan motocin da Sarakunan a shafinsa na Facebook ya bayyana cewa Kansilolin jihar 21 sun yi na'am da yadda yake gudanar da mulkinsa.

Fintiri ya kara da cewa Kansilolin sun jinjina masa bisa ayyukan da yake a bangaren Ilimi, kiwon lafiya, ds.

Gwamnan jihar Adamawa
Gwamnan jihar Adamawa ya rabawa Sarakunan gargajiyar jihar manyan Motoci Hoto: Governor Ahmadu Umaru Fintiri
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

'Yan APC mashaya barasa ne, su suke sukar ayyuka na a Benue, gwamna Ortom

Bugu da kari, Gwamna ya bayyana cewa Kansilolin sun tara masa N22 million don saya masa Fam din takara a zaben fidda gwani karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a 2023.

Yace:

"Yau na raba SUV da Hilux ga dukkan Sarakunan gargajiyanmu masu matsayi na daya."
"Hakazalika Kansilolin kananan hukumomi 21 sun yi amanna da ni kuma sun jinjinawa nasarori na a sashen Ilimi, manyan ayyuka, kiwon lafiya, dss."
"Sun alanta bada gudunmuwan milyan 22 don saya min Fam na takaran zaben Gwamna a 2023."

Asali: Legit.ng

Online view pixel