Bidiyon kwastoma da ya shigo banki da igiya ya yi yunƙurin zai halaka kansa don kuɗin da banki ke cire masa

Bidiyon kwastoma da ya shigo banki da igiya ya yi yunƙurin zai halaka kansa don kuɗin da banki ke cire masa

  • Wani dan Najeriya saboda tsabar damuwar da ta yi masa yawa ya rikita harabar wani banki akan cire-ciren kudaden da suke yi masa
  • Kwastoman cike da fushi ya isa bankin rike da igiya yana ihu da yunkurin zai halaka kansa inda yake cewa sun yashe masa kudadensa tas da ke asusun bankin
  • Nan da nan ma’aikatan bankin tare da wasu kwastomomi su ka fara rokonsa su na kokarin amshe igiyar da ke hannunsa don gudun ya halaka kansa

Wani fusataccen kwastoma ya bayyana cikin wani yanayi wanda yake nuna rashin gamsuwarsa da cire-ciren kudaden da banki ke masa a asusunsa.

Matashin ya bayyana da igiya a hannunsa ya na yunkurin halaka kansa bisa zargin bankin da tura wa barayin yanar gizo kudade daga asusun bankinsa.

Bidiyon kwastoma da ya shigo banki da igiya ya yi yunkurin zai halaka kansa don kudin da banki ke cire masa
Ma'aikatan bankin sun yi gaggawar hana shi yi wa kansa rauni. Hoto: @rootstv.nigeria
Asali: Instagram

Roots TV Nigeria sun wallafa bidiyon yadda lamarin ya auku a shafinsu na Instagram inda yake bayyana cewa bai san yadda aka yi N450,000 ta fita daga asusunsa ba.

Kara karanta wannan

Mota ta farko da zan hau ni zan kera ta : Yaron Najeriya da ya hada mota da karafuna

An samu rahoto akan yadda bankin suka bukaci ya gabatar da takardar kotu wacce zai tabbatar da cewa baya da masaniya akan fitar kudin.

Bayan ya gabatar da takardar kotun bankin su ka ki amincewa da bangarensa sai na barayin yanar gizon.

Ma’aikatan banki tare da kwastomomi sun yi yunkurin hana shi

A bidiyon an ga inda ma’aikatan bankin da wasu kwastomomi su ka tsaya ka’in da na’in wurin kwace igiyar da zai halaka kansa daga hannunsa.

An samu bayanai akan yadda lamarin ya faru a reshen wani banki a jihar Legas, nan da nan ‘yan Najeriya su ka fara tsokaci karkashin bidiyon.

Megarates_crypto ya ce:

“Irin haka ya taba faruwa dani a bankin kuda inda na tura kudi daga zenith zuwa kuda ba tare da ya shiga asusuna ba. Daga baya na gane sharrin barayin yanar gizo ne, sannan naje banki aka gyara min.”

Kara karanta wannan

Hamshakin mai kudi ya gina gidaje 90, ya bada kyautarsu a murnar bikin diyar shi

Euestrellas2017 ya ce:

“Haka bankin UBA su ke yi da gangan. Sun taba yiwa sirikina haka. Katinsa ya makale a wani ATM a cikin kwanakin karshen mako, ranar Talata ya kai musu korafi. Bayan ya cikasa wata takarda sai ga kudin ya dawo.”

Donatusgodwin ya ce:

“Ba yadda ba su yi dani ba a bankin UBA na ce ba zan iya harka da bankin ba. Gara ma in rufe asusun bankin gabadaya.”

Abin da yasa har yanzu Nigeria bata zama ƙasaitacciyar ƙasa ba, Ministan Buhari

A wani labarin daban, Ministan Kimiyya da Fasaha, Ogbonnaya Onu, ya ce har yanzu Nigeria bata cimma babban matakin da ake sa ran ta kai ba a lokacin samun 'yanci saboda an yi watsi da irin halayen mazajen jiya da suka kafa kasar.

Ya yi wannan jawabi ne a babban birnin tarayya Abuja wurin wani taro da kungiyar 'Yan Kabilar Igbo ta shirya don karrama Rear Admiral Godwin Kanu Ndubuisi (mai ritaya), Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yan bindiga da Sojojin sun yi musayar wuta a Imo kan umarnin zama a gida na IPOB

Onu ya ce ya zama dole 'yan Nigeria su zama masu gaskiya, aiki tukuru da riko da halaye na gari idan suna son ganin kasar ta zama tauraro tsakanin sauran kasashe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel