Da duminsa: Yayinda ake gudun Omicron, Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Shugaban kasar Afrika ta Kudu

Da duminsa: Yayinda ake gudun Omicron, Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Shugaban kasar Afrika ta Kudu

  • Shugaban kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa ya kawo ziyarar aiki Najeriya ranar Laraba
  • Ramaphosa ya dira Najeriya bayan kira da Shugabannin duniya su daina kyamatar Afrika kan sabon nau'in Korona
  • Kasashen duniya sun sanya dokar hana shigar yan kasar Afrika ta kudu kasashensu don dakile yaduwar nau'in cutar Korona na Omicron

Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin takwararsa na kasar Afrika ta kudu, Cyril Ramaphosa, ranar Laraba, 1 ga Disamba, 2021 a fadar Aso Villa dake Abuja.

Punch ta ruwaito cewa Cyril Ramaphosa, ya dira Aso Rock ne misalin karfe 10 na safe tare da tawagarsa kuma ya samu kyakkyawar tarba.

A riwayar ChannelsTV, tun daren jiya Ramaphosa ya dira Najeriya kuma ya ci abincin dare tare da Buhari.

Ziyararsa ta biyo bayan sanarwar hukumar kiyaye yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC cewa nau'in cutar Korona, Omicron, ta bulla a Najeriya.

Kara karanta wannan

Ka ceto 'yan Najeriya daga yunwa da rashin tsaro, Agbekoya ga Buhari

Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Shugaban kasar Afrika ta Kudu
Da duminsa: Yayinda ake gudun Omicron, Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Shugaban kasar Afrika ta Kudu Hoto: Presidency
Asali: Twitter

Kasar Kanada ta sa takunkumi ga 'yan Najeriya saboda Omicron

Kasar Kanada ta sanya dokar hana shigar yan Najeriya kasar a wani yunkuri na dakile yaduwar nau'in cutar Korona na Omicron.

Kasar ta Arewacin Amurka da ke samun kwararar bakin haure daga Najeriya ta sanar da hakan ne a safiyar yau Laraba 1 ga watan Disamba.

Ya zuwa yanzu, hukumomin Kanada sun haramtawa kasashe 10 shiga kasarsu saboda bullar sabon nau'in na Korona.

Abin da ya dace a sani kan sabon samfurin COVID-19 Omicron

Omircon ta na rikida har nau’i 32 a jikin Bil Adama, hakan ya nuna ta fi irinsu samfurin Delta ikon rikida, Masana sun ce wannan zai jawo ta gagara jin magani da wuri.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Kasar Kanada ta sa takunkumi ga 'yan Najeriya saboda bullar Korona

An tabbatar da cewa nau’in cutar B.1.1.529 ya fi samufurin Delta sauran yaduwa a tsakanin mutane.

Masana kiwon lafiya ba su iya tabbatar da inda cutar ta fito ba. Abin da aka sani shi ne an fara ganin mai dauke da samufurin ne a ranar 23 ga watan Nuwamba, 2021.

A halin yanzu cutar ta shiga kasashe kusan 20, daga ciki har da Najeriya. Kasashen da aka samu bullar ta sun hada da: Ingila, Kanada, Afrika ta kudu, Denmark da Belgium, dss.

Asali: Legit.ng

Online view pixel