Omicron: Abin da ya dace a sani kan sabon samfurin COVID-19 da ke neman sake rufe kasashe

Omicron: Abin da ya dace a sani kan sabon samfurin COVID-19 da ke neman sake rufe kasashe

  • A ranar 25 ga watan Nuwamba, 2021, hukumar kula da cututtuka masu yaduwa ta kasar Afrika ta kudu (NICD) ta bada sanarwar gano sabon samfurin COVID-19
  • Wannan samfuri na B.1.1.529 wanda daga baya aka yi wa lakabi da Omricon, shi ne ‘dan auta a gidan cutar murar mashako ta Coronavirus da ta bayyana a shekarar 2019
  • Mun kawo wasu daga cikin abubuwan da ya kamata a sani game da wannan nau’in cuta. Tuni dai wasu kasashe suka fara dawo da takunkumin da aka kakaba a baya

The Cable tace hukumar lafiya ta Duniya ta sa wa wannan samfuri suna da Omicron, kuma ta tabbatar da hadarin cutar saboda irin yadda ta ke yawan hayayyafa.

Omicron ta na da hadari?

Omircon ta na rikida har nau’i 32 a jikin Bil Adama, hakan ya nuna ta fi irinsu samfurin Delta ikon rikida, Masana sun ce wannan zai jawo ta gagara jin magani da wuri.

An tabbatar da cewa nau’in cutar B.1.1.529 ya fi samufurin Delta sauran yaduwa a tsakanin mutane.

Daga ina Omicron ta bullo?

Masana kiwon lafiya ba su iya tabbatar da inda cutar ta fito ba. Abin da aka sani shi ne an fara ganin mai dauke da samufurin ne a ranar 23 ga watan Nuwamba, 2021.

Omicron
Ana gudun COVID-19 Hoto: economictimes.indiatimes.com
Asali: UGC

Wasu kasashe cutar ta shiga?

A halin yanzu cutar ta shiga kasashe kusan 20, daga ciki har da Najeriya. Kasashen da aka samu bullar ta sun hada da: Ingila, Kanada, Afrika ta kudu, Denmark da Belgium.

CNN tace wannan cutar ta shiga kasashen Hong Kong, Botswana, Israila, Jamus da Australia. Sai Austriya, Czech, Faransa, Jafan, Italiya, Suwidin, Holand da kasar Fotugal.

Jinyarta ta sha bam-bam?

Wani rahoto na gidan talabijin na Aljazeera yace har yanzu babu abin da ke nuna cewa masu jinyar Omicron sun sha bam-bam da sauran wadanda COVID-19 ta harba.

An samu maganin Omicron?

Kamfanin BioNTech sun ce za a dauki lokaci kafin a san ko magungunansu zai yi aiki a kan masu dauke da Omicron. Za a dauki akalla mako kafin a gama wannan bincike.

Su ma kamfanin Moderna su na gwaji domin su inganta magungunan da suka yi a baya domin a yaki sabon samufurin wannan cuta wanda ya ke ta harbin mutane a Duniya.

Ya ake yin gwajin B.1.1.529?

Rahoton yace ana iya gano kwayar wannan samufuri kamar yadda ake yin sauran gwajin COVID-19.

Omicron ta shigo Najeriya?

A yau ne hukumar dakile cututtuka masu taduwa a Najeriya ta NCDC ta tabbatar da bullar nau'in cutar COVID-19 na Omicron da yanzu ya ke ta kewaye kasashen duniya.

Hukumar ta ce bayan gwaji, an gano mutane biyu da ke dauke da nau'in cutar a halin yanzu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel