Da Dumi-Dumi: Abin da na faɗa wa Nnamdi Kanu da na kai masa ziyara a yau, Bulaliyar Majalisa, Kalu

Da Dumi-Dumi: Abin da na faɗa wa Nnamdi Kanu da na kai masa ziyara a yau, Bulaliyar Majalisa, Kalu

  • Bulaliyar Majalisar Tarayya, Sanata Orji Kalu ya ziyarci Shugaban IPOB, Nnamdi Kanu da ke tsare a ofishin DSS a birnin tarayya Abuja
  • Tsohon gwamnan na Abia ya ce duk da ra'ayinsu sun banbanta, Kanu, dan uwansa ne don haka ba zai yi watsi da shi ba
  • Kalu ya ce ya shawarci Nnamdi Kanu ya rika nazarin abin da zai faru da mutanensa kafin ya rika furta maganganu da ka iya tada zaune tsaye

Abuja - Bulaliyar Majalisar Tarayyar Najeriya, a ranar Litinin, ya ziyarci shugaban haramtaciyyar kungiyar masu neman kafa Biafra, IPOB, Nnamdi Kanu, wanda a yanzu yana hannun DSS.

Tsohon gwamnan na jihar Abia, Kalu, cikin sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook ya ce Kanu na cikin koshin lafiya.

Kara karanta wannan

NDLEA: Matar da aka cafke ta hadiyi ledoji 80 na Koken, ta yi kashin su a filin jirgi

Da Dumi-Dumi: Abin da na faɗa wa Nnamdi Kanu da na kai masa ziyara a yau, Bulaliyar Majalisa, Kalu
Orji Uzor Kalu ya ziyarci Nnamdi Kanu da ke tsare hannun DSS. Hoto: The Nation
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kalu ya ce ya yi magana da Kanu a matsayin dan uwa ya kuma fada masa bukatar da ke da akwai ya rika yin tunanin abin da zai biyo baya kafin ya dauki mataki kan lamura.

Ya ce duk da cewa ra'ayins da na Kanu sun banbanta, zai cigaba da ba shi shawara a matsayin dan uwa.

A sanarwar da ya wallafa a shafinsa na Facebook, a cewar sanarwar da hadiminsa, Kenneth Cole, ya fitar a Abuja, Kalu ya ce:

"A yau da rana, na ziyarci dan uwa na, Mazi Nnamdi Kanu da ke hannun DSS a Abuja.
"Na tara da shi cikin koshin lafiya kuma mun yi tattauna abubuwa a matsayin mu na 'dan uwa'
"A shekara 2001 lokacin ina gwamna, na nada mahaifinsa Eze Isreal Okwu Kanu sarautar Akwara Ukwu kuma tun lokacin zumunci ya kullu tsakanin mu.

Kara karanta wannan

Limamin Kiristanci ya roki FG da ta yafe wa Nnamdi Kanu da sauransu laifukansu

"Na san cewa yana da magoya baya sosai a gida kuma ina rokonsa ya rika duba abin da zai same mutanensa sakamakon abubuwan da ya ke furtawa.
"Duk da ra'ayin mu sun sha banban, Allah ya yi mu yan uwa kuma ba za mu iya canja hakan ba.
"Haki na ne in bashi shawara da sauran yan Nigeria ko da shi da iyalansa za su saurara ko ba za su saurara ba. Zan cigaba da bashi shawara kamar yadda na saba. Abin da muke so shine zaman lafiya."

Tunda DSS ta kama Nnamdi Kano tsawon watanni, ba ta bar shi ya sauya tufafi ba, Lauyansa

A wani labarin, lauyan shugaban kungiyar masu rajin kafa kasar Biafra ta IPOB, Ifeanyi Ejiofor, ya ce tunda jami’an tsaro na fararen kaya, DSS su ka kama Nnamdi Kanu, ba su bar shi ya sauya suttura ba.

A wata takarda wacce The Cable ta ruwaito lauyoyin Kanu, Ejiofor da Aloy Ejimakor sun sa hannu ranar Alhamis, sun bayyana cewa DSS ta na matukar cutar da Kanu.

Lauyoyin sun ce yanzu haka hukumar azabtar da duk mazaunin kurkukun da ya yi magana da Kanu tare da horar da shi saboda gaisuwa da ya yi da shugaban IPOB din, The Cable ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel