Jihar Gombe ta fi ko wacce jiha a Najeriya talauci, cikin mutum 10, 7 talakawa ne tilis - UNICEF

Jihar Gombe ta fi ko wacce jiha a Najeriya talauci, cikin mutum 10, 7 talakawa ne tilis - UNICEF

  • Majalisar dinkin duniya ta tallafa wa yara, UNICEF ta ce jihar Gombe ta fi ko wacce jiha a Najeriya fama da fatara ta kaso 74.6 bisa dari
  • Bisa bincike, idan aka ware mutane goma mazauna jihar, bakwai cikinsu duk talakawa ne tilis, Yusuf Auta, masani a harkar kariyar zamantakewa ya shaida hakan a wani taro
  • Ya kara da bayyana cewa yara da mata a jihar ba sa samun ingantaccen ilimi, muhalli, sutura, kayan masarufi da sauran kayan more rayuwa

Plateau, Jos - Asusun tallafawa yara na majalisar dinkin duniya, UNICEF, ta ce kaso 74.6 cikin 100 na mazauna jihar Gombe duk talakawa ne, The Cable ta ruwaito.

Yusuf Auta, masani a harkar kariyar zamantakewa karkashin UNICEF a ofishinta na jihar Bauchi ya yi wannan jawabin a wani taro na tsarin ci gaban jihar Gombe ranar Litinin a Jos.

Kara karanta wannan

Rundunar soji ta kame jami'anta da suka ci zarafin wasu mazauna a yankin Abuja

Jihar Gombe ta fi ko wacce jiha a Najeriya talauci, cikin mutum 10, 7 talakawa ne tilis - UNICEF
Taswirar jihohin Nigeria. Hoto: The Nation
Asali: UGC

Auta ya bayyana yadda aka samu wannan bayanin yayin bincike akan kariya ta zamantakewa na jihar, Daily Nigerian ta ruwaito.

“Bincike ya nuna yadda kaso 74.6 cikin 100 na mazauna jihar Gombe suke rayuwa cikin talauci da fatara.
“An kiyasta cewa mutane 7 cikin 10 na mazauna Gombe talakawa ne,” a cewarsa.

Yara kanana a jihar su na rayuwa cikin kuncin rayuwa

Auta ya koka akan yadda yara kanana dake zama a jihar su ke rayuwa cikin talauci.

A cewarsa hakan ya na nuna cewa yara da dama da ke zama a jihar ba sa samun damar cin abinci mai kyau, asibiti mai kyau, ilimi ingantacce, muhalli, ruwa da hanyoyin sadarwa.

Ya yaba wa gwamnatin jihar akan samar da hanyar ci gaban jihar inda yace hakan zai taimaka wa ci gaba da bunkasar jihar.

Kara karanta wannan

'Kuncin rayuwa ta tunzura ni: Matashin da aka kama da hodar iblisa ta N2.7bn a filin jirgin Abuja

Ya ce in har aka bi hanyoyin da suka dace yara da matan da ke zama a jihar zasu more rayuwa.

UNICEF na farincikin tallafa wa yara da mata

Ya kara da bayyana cewa UNICEF tana farincikin kasancewa cikin tsarin da zai tallafa wa rayuwar yara da mata.

Kuma dama UNICEF ta fi mayar da hankali akan matsalolin mata da na yara.

Tsarin kariyar zamantakewa zai tallafa wa mata da yara don samun ingantacciyar rayuwa kamar yadda Auta ya shaida.

A cewarsa:

“Mun zo ne don tabbatar da tsarin da zai tallafa wa jihar.”

Kuma UNICEF ta sha alwashin ci gaba da taimaka wa jihar wurin shawo kan matsaloli don samun nasarori.

NAN ta ruwaito yadda taron ya samu halartar mutane daban-daban na ma’aikatun gwamnati, bangarori, kungiyoyi, MDAs, shugabannin gargajiya, abokan ci gaba, manema labari da sauransu.

Ana bin kowanne ɗan Najeriya bashin N64,684 bisa basukan da ƙasar ta ci a ƙasashen waje

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna ga PDP: Ku bar tikitin shugaban kasa a zaben 2023 ga mai rabo

A wani labarin, kun ji cewa bisa yawan ‘yan Najeriya da kuma yawan basukan da ake bin ta, kowa ya na da N64,684 a kan sa.

Kamar yadda kowa ya san yawan bashin da Najeriya take ta amsowa daga kasashen ketare, yanzu ko wanne dan Najeriya ya na da bashin $157 ko kuma N64,684 a kan sa.

Bisa wannan kiyasin, masanin tattalin arzikin kasa, Dr. Tayo Bello ya bayyana damuwar sa akai inda ya ce duk da zuzurutun basukan, babu wasu abubuwan ci gaba da aka samar wadanda za su taimaka wurin biyan basukan kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel