'Kuncin rayuwa ta tunzura ni: Matashin da aka kama da hodar iblis ta N2.7bn a filin jirgin Abuja

'Kuncin rayuwa ta tunzura ni: Matashin da aka kama da hodar iblis ta N2.7bn a filin jirgin Abuja

  • Hukumar yaki da fasa kwaurin miyagun kwayoyi ta NDLEA ta bayyana yadda ta damki Maduabuchi Chinedu da kilograms 9.30 na hodar ibilis
  • Hodar ibilis din da aka kama Chinedu da ita ta kai kimar naira biliyan 2.7 a cikin filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe da ke birnin tarayya, Abuja
  • Kakakin hukumar, Femi Babafemi ne ya bayyana hakan ta wata takarda wacce yace an kama matashin mai shekaru 32 a ranar 24 ga watan Nuwamba

Abuja - Hukumar yaki da fasa-kwaurin miyagun kwayoyi, NDLEA, ta yi kama wani Maduabuchi Chinedu da hodar ibilis kilo gram 9.30 da kudinsa ya haura Naira biliyan 2.7 a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe, Abuja.

Jaridar The Cable ta rahoto yadda kakakin hukumar a ranar Alhamis, Femi Babafemi ya sanar da kamun matashin mai shekaru 32.

Kara karanta wannan

N2.3tr muka ware don rabawa yan Najeriya kayan tallafin Korona, Gwamnatin tarayya

NDLEA ta kama hodar iblis ta N2.7bn a filin jirgin Abuja
An kama wani matashi da hoda iblis a filin jirgin Abuja. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

A cewarsa an kama wanda ake zargin wanda mazaunin Liberia ne yayin binciken masu wucewa Ethopia a filin jirgin a ranar 24 ga watan Nuwamba.

Babafemi ya ce wanda ake zargin dan asalin kauyen Obaha Okigwe a karamar hukumar Okigwe da ke jihar Imo ya na aiki ne a wurin ma’adanai a Liberia, rahoton The Cable.

Kakakin ya ce hodar ibilis din mai nauyin kilo gram 9.30 ya adana ta ne a wani daurin minti wanda ya boye a cikin jakar kayansa.

Chinedu ya ce kuncin rayuwa ne ya kaishi ga sayar da miyagun kwayoyi

Yayin hira da shi, Chinedu ya bayyana yadda ya bar Najeriya ya koma zama a Liberia inda ya koma can dindindin.

Takardar ta bayyana cewa :

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: EFCC ta sanya gwamnan Anambra a jerin sunayen wadanda take nema

“Chinedu ya ce kunci da talaucin da yake fama da shi yasa ya yanke shawarar neman kudi don tallafa wa mahaifiyarsa da ke fama da ciwon idanu.
“Daga nan ya ce wani abokinsa a Liberia ya ba shi hodar ibilis din don ya kai wa wani mazaunin Adis Ababa, Ethopia a naira miliyan daya.
“Ya kara da cewa da farko zai wuce da hodar ne Ivory Coast amma sai aka kawo shi Najeriya.”

Abin da yasa Legas ta zama matattaran mashaya, muggan ƙwayoyi, Kakakin Majalisa Obasa

A wani labarin, kakakin majalisar jihar Legas, Mudashiru Obasa, ya yi alkawarin cewa majalisar jihar za ta cigaba da goyon bayan yakin da ake yi da shan miyagun kwayoyi a jihar da illar da hakan ke yi wa matasa da mazauna jihar.

A ruwayar The Punch, Obasa ya yi wannan alkawarin ne yayin da ya karbi bakuncin jami'an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA, da kwamandan jihar, Ralph Igwenagu ya yi wa jagoranci.

Kara karanta wannan

Abun bakin ciki: Jam’iyyar PDP ta sake rashi na wani babban jigonta

Kakakin majalisar ya ce yana fatan idan aka hada hannu wurin yaki da matsalar hakan zai taimaka wurin inganta lafiyar mutanen Legas.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel