Duniya ba tabbas: Iyalin tsohon Gwamnan Sokoto sun saida tsagin gidansa domin su rayu

Duniya ba tabbas: Iyalin tsohon Gwamnan Sokoto sun saida tsagin gidansa domin su rayu

  • A shekarar 1981 Muhammadu Shehu Kangiwa ya rasu ya na kan kujerar gwamnan jihar Sokoto
  • A yau, iyalin da ya bari su na cikin wani hali maras dadi, gwamnatin jihar Sokoto ta manta da su
  • Har yanzu ba a biya iyalin tsohon gwamnan hakkokinsu ba, shekara 40 da rasuwarsa a wajen folo

Sokoto - A halin yanzu, iyalin Marigayi Alhaji Muhammadu Shehu Kangiwa su na zama a gidan benensa ne tare da wasu mutanen a unguwar GRA, jihar Sokoto.

Wani rahoto da jaridar 21st Century Chronicle ta fitar a ranar Litinin, 29 ga watan Nuwamba, 2021, ya nuna yadda halin da iyalin tsohon gwamnan su ke ciki.

Shekaru sama da arba’in kenan rabon da a gyara wannan gida da tsohon gwamnan Sokoto ya zauna a ciki. Wannan gida ya yi raga-raga, ciyayi sun tsiro ko ta ina.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya bayyana yadda 'yan bindiga suka fi gwamnati son ganin karshen ta'addanci

Halin rayuwa a yau

Da 21st Century Chronicle ta samu tayi hira da iyalin marigayin da kyar, ‘dansa Ahmad Shehu Kangiwa ya bayyana cewa mahaifinsu bai bar tarin dukiya ba.

Ahmad Shehu Kangiwa yake cewa gwamna Kangiwa ya bar suna mai kyau, amma bai bar dukiya a Duniya ba, wanda a ganinsa wannan shi ne mafi muhimmanci.

Abin da su ke samu daga gwamnati shi ne buhunan hatsi idan lokacin azumi ya zo, da kudi da ragunan layya a duk lokacin bikin idi a cewar Ahmad Kangiwa.

Tsohon Gwamnan Sokoto
Gidan Shehu Kangiwa Hoto: 21stcenturychronicle.com
Asali: UGC

Shekara 40 ba a fito da hakkin Kangiwa ba

‘Dan autan tsohon gwamnan yace har yanzu iyalin Kangiwa ba su karbi hakkokin mahaifinsu bayan mutuwarsa ba. Ana maganar sama da shekaru 40 kenan.

Ahmad Kangiwa yace ya taba zuwa ma’aikatar fansho ya na neman hakkinsu, amma aka ce ba za a biya kudin ba sai majalisar dokokin jihar Sokoto ta yi doka a kai.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: EFCC ta sanya gwamnan Anambra a jerin sunayen wadanda take nema

“Amma mun fahimci gwamnatin jiha ta biya magajinsa, Alhaji Garba Nadama wanda ya yi masa mataimaki, da kuma tsohon gwamna Yahya Abdulkareem.”
“Mu na rokon gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya kawo mana agaji.” - Ahmad Shehu Kangiwa

A cikin ‘ya ‘yan da tsohon gwamnan ya bari, babu wanda gwamnati ta dauki nauyin karatunsa. Uwayensu ne suka biya masu kudin karatu har zuwa jami'a.

Muhammadu Shehu Kangiwa wanda ya zama gwamnan tsohuwar Sokoto mai hade da Sokoto, Kebbi da Zamfara a 1979 ya rasu ne a wajen wasan folo a 1981.

A ‘dan lokacin da Marigayi Shehu Kangiwa yake gwamna, an samu cigaba sosai a jihar Sokoto. Amma yanzu an bar iyalinsa su na fama da wahalhalun rayuwa.

A shekarar bara aka ji shi ma, magajinsa watau tsohon gwamna Garba Nadama, Allah ya yi masa rasuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel