Bayan kusan shekaru 2 suna zaune gida suna diban albashi, Gwamnati tace ma'aikatanta su koma aiki

Bayan kusan shekaru 2 suna zaune gida suna diban albashi, Gwamnati tace ma'aikatanta su koma aiki

  • Kwamitin fadar shugaban kasa ta yaki da annobar Korona ta yi kira ga dukkan ma'aikatan gwamnati su koma bakin aiki
  • Wannan umurni ya zo daga bakin Shugabar ma'aikatan gwamnatin tarayya, Dr Folasade Yemi-Esan
  • Dr Yemi-Esan ta yi tsokacin cewa wajibi ne duk ma'aikacin gwamnatin da ke niyyar komawa ofis yayi rigakafin Korona

Abuja - Bayan watanni 20 suna zaune a gida tun bullar cutar Korona a Najeriya, gwamnatin tarayya ta ce ma'aikata dake daraja Level 12 da abinda yayi kasa su koma bakin aiki ranar 1 ga Disamba, 2021.

Shugabar ma'aikatan gwamnatin tarayya, Dr Folasade Yemi-Esan ta bayyana hakan a takardar da ta saki mai lamba HCSF/ 3065/ Vol. 1/ 107 da ranar wata, 26 ga Nuwamba, 2021, This Day ta ruwaito.

Ta bayyana cewa bisa shawarar Kwamitin fadar shugaban kasa ta yaki da annobar Korona, Shugaba Buhari ya wajabtawa dukkan masu niyyar dawowa yin rigakafin Korona.

Kara karanta wannan

Garba Shehu: Buhari ya cancanci jinjina kan yadda ya shawo kan matsalar tsaro

Zaku tuna cewa tun watan Maris 2020, gwamnatin tarayya ta umurci ma'aikatan gwamnati masu darajar Lv12 da abinda yayi kasa su rika aiki daga gida domin rage yaduwar cutar.

Gwamnati tace ma'aikatanta su koma aiki
Bayan kusan shekaru 2 suna zaune gida suna diban albashi, Gwamnati tace ma'aikatanta su koma aiki Hoto: Presidency
Asali: Twitter

Duk ma'aikacin da bai yi rigakafin Korona ba nan da kwanaki 10 ba zai shiga Ofis ba

Gwamnatin tarayya ta jaddada cewa duk ma'aikacin gwamnatin da bai yi rigakafin Korona nan da ranar 1 ga Disamba ba, ba zai samu damar shiga ofishinsa ba.

Sakataren Gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya bayyana hakan ranar Juma'a a Abuja yayin taron kamfen yiwa mutane rikakafin.

Ya yi kira ga ma'aikatan gwamnati su ribaci kwanaki goma da suka rage cikin watan Nuwamba wajen yin rigakafin

Adadin wadanda aka yiwa rigakafi kawo yanzu

Kara karanta wannan

Atiku ya ba APC shawara ta dauki kwas a wajen Gwamonin PDP, ya caccaki duka Jihohin APC

Shugaban hukumar cigaban kananan asibitoci (NPHCDA), Dr Faisal Shuaib, ya bayyana adadin yan Najeriya da aka yiwa rigakafi kawo yanzu.

A cewarsa, kawo ranar 19 ga Nuwamba, yan Najeriya 5,989,480 suka yi allurar farko, yayinda mutum 3,341,094 suka yi alluran biyu gaba daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel