Karyar takunkumi Gwamnati ke yi, Sanatoci sun gano ana daukar yaran manya aiki a boye

Karyar takunkumi Gwamnati ke yi, Sanatoci sun gano ana daukar yaran manya aiki a boye

  • Kwamitin majalisar dattawan Najeriya yace ya gano ana daukar mutane aiki ta karkashin kasa har yanzu
  • Shugaban kwamitin, Sanata Danjuma La’ah ya soki ‘karyar’ da ake yi na cewa an sa takunkumin bada aiki
  • ‘Dan majalisar yace babu inda aka ce a daina daukar aiki, ya yi kira a ba matasa abin yi a kasar nan

Abuja - A ranar Laraba, 24 ga watan Nuwamba, 2021, majalisar dattawan Najeriya ta bayyanawa Duniya cewa ana daukar ‘ya ‘yan manya aiki ta bayan-fage.

Vanguard ta rahoto cewa Sanatoci sun koka a kan wannan danyen aiki da ake yi a lokacin da aka sanar da kowa cewa an sa takunkumin daukar aiki a gwamnati.

‘Yan majalisa sun yi tir da wannan lamari, sannan suka kalubalanci jami'an gwamnatin tarayya su nuna hujjar da ke nuna an dakatar da daukar aikin gwamnati.

Kara karanta wannan

Abin da ya sa Gwamnati ba ta isa ta rabawa Talakawa kudi idan an cire tallafi ba - ‘Yan Majalisa

Shugaban kwamitin daidaiton mukaman gwamnatin tarayya a majalisa, Sanata Danjuma La’ah ya bayyana wannan a lokacin da yake gabatar da rahotonsu a jiya.

Jaridar tace kwamitin da La’ah yake jagoranta ya mika rahoton aikin da suka yi kan kasafin kudin shekarar 2022 mai zuwa ga kwamitin kasafi na majalisa.

Sanatoci
Zauren Majalisar Dattawa Hoto: NgrSenate
Asali: Facebook

Abin da Sanata La'ah ya fada

“Ban san ina suka samo wannan ba. Mu na ta tambayarsu. Babu wani takunkumi a ko ina.”
“Wasu jami’an gwamnati ba su da hangen nesa, su na amfani da wannan dama.” – La’ah.

A nemawa matasa abin yi a kasa

“Yanzu lokaci ne da za su kara yawan abin da suke kashewa, su samar da ayyukan yi.” – La’ah.
“Mutane su na ritaya da kansu, amma ba mu san yadda ake maye gurabensu (a gwamnati) ba. Dole ne mu san adadin muttanen da ake nema domin a ba aiki.”

Kara karanta wannan

Rigima ta nemi ta kaure a taron Gwamnonin APC, sai da Shugaban Gwamnoni ya tsoma baki

“Mun gano akwai matasan da suka gama karatu a manyan makaranta shekaru kimanin 15 da suka wuce, amma har yau ba su samu wani aikin yi ba. – La’ah.

Sanatan yake cewa ya kalubalanci masu daukar aiki a boye, su nuna masa inda suka samu bayani daga gwamnati cewa an ce a dakatar da daukar mutane aiki.

Kwanaki Ministan kwadago da samar da ayyukan yi na kasa, Dr. Chris Ngige, ya yi bayanin abin da ya sa aka daina daukar sababbin ma’aikata a gwamnatin tarayya.

La’ah mai wakiltar yankin kudancin jhar Kaduna a karkashin jam’iyyar PDP yace an dauki mutane da-dama aiki a lokacin da ake cewa an sa takunkumi a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel