Dalilinmu na daina daukar sababbin ma’aikata aiki a Gwamnati inji Ministan kwadago

Dalilinmu na daina daukar sababbin ma’aikata aiki a Gwamnati inji Ministan kwadago

  • Sarkin Nnewi, Kenneth Orizu ya kai wa Sanata Chris Ngige ziyara a gidansa
  • Mai martaba ya roki Ministan ya taimakawa mutanensu da aiki a gwamnati
  • Chris Ngige yace halin tattalin arziki ya sa aka dakatar da daukar ma’aikatan

Abuja - Ministan kwadago da samar da ayyukan yi a kasa, Sanata Chris Ngige, ya yi bayanin abin da ya sa aka daina daukar ma’aikata a gwamnatin tarayya.

Jaridar The Nation ta rahoto Sanata Chris Ngige ya na cewa halin da tattalin arzikin Najeriya ya shiga a halin yanzu ne ya jawo suka dauki wannan mataki.

Ministan wanda ya na cikin kwamitin da ke kokarin farfado da tattalin arziki, yace sun samar da hanyoyin da tsare-tsaren da za su taimaka wa marasa karfi.

Igwe Kenneth Orizu ya ziyarci Chris Ngige

Kamar yadda Punch ta bayyana, Dr. Chris Ngige ya bayyana haka ne a lokacin da ya gana da Sarkin Nnewi, Igwe Kenneth Orizu (III), da ya kai masa ziyara.

Kara karanta wannan

Sanusi II: Najeriya ba ta cimma komai ba cikin shekaru 40, dole na fadi gaskiya

Ofishin yada labaran Ministan kwadagon ya fitar da jawabi, yana mai maida martani ga manyan da suka nemi alfarma a nema wa ‘ya ‘yansu abin yi a gwamnati.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ministan kwadago
Chris Ngige da Muhammadu Buhari Hoto: www.lindaikejisblog.com
Asali: UGC

“Gwamnatin tarayya ta sa takunkumi a kan daukar aiki ne saboda tattalin arzikinmu ba daidai yake ba.”
“Amma mun kawo tsare-tsaren bada tallafi kamarsu CCT da ake raba kudi ga marasa galihu da sauransu. Ana raba wadannan kudi ne ga talaka wa a gari.”
“Ina kokarin ganin garin Nnewi sun samu kasonsu ta sanadiyyar mutanena da na ke da su. Ba ya kadan, amma na tabbatar maku cewa za mu kara kokari.”

Mai girma Ministan ya yi wa ‘yan Najeriya alkawari, har da mutanen Nnewi cewa da zarar gwamnatin tarayya ta cire takunkumi, za a ba al’umma aiki.

Da yake jawabi a gaban mai martaban, Dr. Ngige ya yi alkawari za a inganta halin da babban asibitin koyon aiki na jami’ar Nnamdi Azikiwe yake ciki a yau.

Kara karanta wannan

Sanatan Borno ya ja-kunnen Sojoji a kan maida tsofaffin ‘Yan ta’addan Boko Haram ‘yan lele

Sanatan Borno ta Kudu, Ali Muhammad Ndume ya ja-kunnen sojoji kan maida tsofaffin ‘Yan ta’addan Boko Haram ‘yan lele da ake yi a yankin Arewa maso gabas.

‘Dan majalisar dattawan kasar ya gargadi sojoji cewa su yi hattara sosai da ‘yan ta’addan da suke mika kansu, yace ya kamata a binciki tsofaffin mayakan ne a tsanake

Asali: Legit.ng

Online view pixel