EFCC: Ma’aikacin banki ya tona yadda tsohon gwamna da SGG suka 'ci' N1.5bn a 2015

EFCC: Ma’aikacin banki ya tona yadda tsohon gwamna da SGG suka 'ci' N1.5bn a 2015

  • Tsakanin Junairu da watan Mayun 2015, Jonah Jang ya cire kusan Naira biliyan 2 a asusun banki
  • Wani shaida da lauyoyin EFCC suka gabatar ya bayyana haka a shari’ar da ake yi da tsohon gwamnan
  • Wani ma’aikacin banki ya shaidawa Alkali yadda a lokaci guda aka cire biliyoyin kudi daga asusu

Plateau - Wani mai bada shaida da hukumar EFCC ta dauko, Emmanuel Kpanja, ya shaidawa kotu yadda Jonah Jang ya dauki Naira biliyan 1.9 a watanni biyar.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa, an koma babban kotun jiha da tsohon gwamnan Filato, Jonah Jang, har lauyoyin EFCC sun fara gabatar da shaidunsu.

Wanda hukumar EFCC ta kawo domin ya bada shaida, wani ma’aikacin banki ne da yake zaune a a sashen Bukuru, a karamar hukumar Jos ta Kudu, jihar Filato.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: EFCC ta sanya gwamnan Anambra a jerin sunayen wadanda take nema

Emmanuel Kpanja ya fadawa Alkali Christine Dabup cewa a watan Maris na 2015, tsohon gwamnnan ya hada-kai da Yusuf Gyang Pam, sun lakume N370m.

Yusuf Gyang Pam shi ne akawun sakataren gwamnatin jihar Filato a lokacin da Jang yake gwamna. Jaridar nan ta Daily Nigerian ta tabbatar da wannan rahoto.

Jonah Jang
Sanata Jonah Jang Hoto: @EFCCNigeria
Asali: Facebook

An jefi Jang da SSG da laifuffuka 17

Laifuffuka 17 ke kan wuyan Jonah Jang da Yusuf Gyang Pam. Daga cikin zargin da ake yi masu akwai cin amana, karkatar da kudi, da wawurar Naira biliyan 6.3.

Da aka shiga kotu a ranar Laraba, 24 ga watan Nuwamba, 2021, wanda EFCC ta kawo domin ya bada shaidansa ya yi amfani da takardun banki wajen kafa hujjoji.

Wannnan ma’aikacin bankin da ya bada shaida a kotu, yace a watan Maris na shekarar 2015 ne Pam ya zari Naira miliyan 36.8 daga asusun bankinsu a jihar Filato

Kara karanta wannan

An shirya tsaf, saura kiris a kawo Sunday Igboho Najeriya don ya fuskanci hukunci

Tsakanin Junairu da Mayun 2015, yace akawun na SSG ya cire N7.5m, N3m, N165m, N25m, N60m, N160m, N142m, N974.168m, da N260m daga asusun bankinsu a Bukuru.

Kpanja ya kuma ce a ranar 16 ga watan Maris kuma, Yusuf Pam ya sake cire Naira miliyan 550. Ma’aikacin bankin yace akawun ya cire kudin a cikin sahu takwas.

PDP a zaben 2023

Umar Sani yace jam’iyyar PDP ta samu rabuwar kai sosai a jihar Kaduna, har ta barke zuwa gidaje uku, don haka aka ji yana cewa da wuya su iya lashe zabe a 2023.

Jigon na Jam’iyyar PDP yace ddan aka yi sake, ba za su iya doke APC a zabe mai zuwa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel