Allah kada ka bari yunwa ya halaka Najeriya: Jarumar fim ta yi addu’a yayin da farashin kwai 1 ya kai N90

Allah kada ka bari yunwa ya halaka Najeriya: Jarumar fim ta yi addu’a yayin da farashin kwai 1 ya kai N90

  • Jarumar masana'antar shirya fina-finan kudu wato Nollywood, Uche Elendu ta koka a kan tsadar rayuwa da ake fama da ita a kasar
  • Elendu ta roki Allah da ya ceci bayinsa kada ya bari yunwa ya lalata kasar Najeriya
  • Ta yi al'ajabin cewa idan har za a siyar da kwai guda daya kan N90, toh nawa za a siyar da kazar da ke saka kwan

Shahararriyar jarumar masana'antar shirya fina-finan kudu wato Nollywood, Uche Elendu ta koka a kan tsadar rayuwa a kasar.

Jarumar ta nuna al'ajabi kan farashin da ake siyar da kwai kwaya daya a yanzu wanda yake a kan N90.

Allah kada ka bari yunwa ya halaka Najeriya: Jarumar fim ta yi addu’a yayin da farashin kwai 1 ya kai N90
Allah kada ka bari yunwa ya halaka Najeriya: Jarumar fim ta yi addu’a yayin da farashin kwai 1 ya kai N90 Hoto: @ucheelendu, @theguardian
Asali: Instagram

Elendu ta roki Allah a kan kada ya bari yunwa ya halaka Najeriya, inda ta nuna mamakinta kan cewa idan har ana siyar da kwai kan N90 toh nawa za a siyar da kazar da ke yin kwan kenan.

Kara karanta wannan

Dan Najeriya ya maka MTN a kotu kan cire masa N50, an biya shi N5.5m diyya

'Yar wasar ta kuma nuna tausayawanta ga talakawan Najeriya wadanda suka tsinci kansu a cikin wani irin yanayi na tsada da wahalar rayuwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda lindaikejiblogofficial ta nakalto, Uche ta wallafa a shafin nata cewa:

"Kwai ya zama naira 90??? Ya Allah ka taimaki bayinka, Kada ka bari yunwa ya lalata Najeriya.. Kwai ya zama sai wane da wane? Toh nawa kenan za a siyar da kazar da ke saka kwan?? Ina ji wa al'umma tsoro."

Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin martanin jama'a kan wannan al'amari.

lachantel_cosmetics_chanbeauty ta ce:

"Shin muna iya magana game da man gyada #abun bakin ciki"

tseju_hair1 ta ce:

"Ba wai matsalar talakawa ba kawai...saboda idan yunwa yayi yawa laifuka za su karu wanda zai dawo ya shafi kowa"

mizz_dorah ta yi martani:

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya ta amincewa kamfanonin wuta su kara kudin shan lantarki a 2021

"Nagode Allah bana cin kwai"

Farashin litan man fetur zai iya tashi N170, Yan kasuwar

A wani labari na daban, mun ji cewa da yiwuwan farashin litan man fetur ya tashi daga N165 zuwa N175 yayinda farashin ex-depot zai tashi daga N159 zuwa N165, yan kasuwar mai sun bayyana ranar Alhamis.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa kungiyar yan kasuwan mai masu zaman kansu IPMAN da kuma kungiyar dillalan mai a Najeriya PETROAN sun yi gargadin hakan muddin ba'a dau mataki ba.

Yan kasuwan sun yi korafin karancin mai wanda hakan ya tilastawa masu ajiyar mai kara farashin lita daga N148 zuwa N159.

Asali: Legit.ng

Online view pixel