Dan Najeriya ya maka MTN a kotu kan cire masa N50, an biya shi N5.5m diyya

Dan Najeriya ya maka MTN a kotu kan cire masa N50, an biya shi N5.5m diyya

  • Dan Najeriya mai suna Emmanuel Anenih ya maka kamfanin sadarwa na MTN a gaban kotu kan cire masa N50 inda suka saka masa wakar kira duk da bai bukata ba
  • Kamfanin sadarwa na MTN ya amsa cire masa kudin amma sun tura masa N700 kyauta kan shekaru takwas da yayi yana amfani da layinsa
  • Sai dai alkali Ishaq Bello a hukuncinsa, ya bukaci a biya Anenih N5 miliyan na katse masa jin dadi da aka yi da kuma N500,000 na kudin shari'a da ya kashe

FCT, Abuja - Wani dan Najeriya mai suna Emmanuel Anenih a watan Oktoban 2014, ya maka kamfanin sadarwa na MTN a gaban kotu kan cire masa naira hamsin da aka yi kuma aka saka masa wakar kira duk da bai bukata ba.

Kara karanta wannan

Shugabancin 2023: Gwamna Umahi ya magantu a kan fastocin yaken neman zabensa da suka bayyana

Kamar yadda shafin @naija_reporter suka ruwaito, bayan fafatawa da aka yi tsakanin Emmanuel na kamfanin MTN, ya samu galaba a shari'ar inda kotu ta umarci MTN da ta biya shi makuden kudi.

Dan Najeriya ya maka MTN a kotu kan cire masa N50, an biya shi N5.5m diyya
Dan Najeriya ya maka MTN a kotu kan cire masa N50, an biya shi N5.5m diyya. Hoto daga Daily Trust
Asali: Facebook

A yadda ta kaya a kotun, bayan da alkali ya tabbatar da samun shaidu gamsassu cewa an cutar da shi, an yankewa kamfanin sadarwa na MTN hukunci.

A wata wasika da MTN ta tura wa wanda yayi kara, ta aminta cewa ta kwashe masa kudin inda ta saka masa wakar da mai kiransa zai ji duk da bai bukata ba.

Amma kuma daga bisani, ta tura masa kyautar N700 na kira ga wanda yayi kara kan shekaru takwas da yayi yana amfani da layinsa bayan yayi korafin.

Babban alkalin kotun, Mai shari'a Ishaq Bello a hukuncinsa, ya ce dari bakwan da aka tura masa bata kai diyyar katsewa mai karar jin dadinsa da aka yi ba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya ta amincewa kamfanonin wuta su kara kudin shan lantarki a 2021

Kotun daga nan ta umarci kamfanin sadarwa na MTN da ta biya shi naira miliyan biyar na barnar da ta yi masa wurin katse masa zaman lumanarsa ta hanyar saka masa wakar da masu kira za su ji ba tare da ya bukata ba.

Har ila yau, kotun ta bukaci kamfanin sadarwa na MTN da ta kara masa naira dubu dari biyar na kudaden da ya kashe wurin shari'a.

Labarin rigar mama ta lu'u-lu'u a kayan Diezani: Shugaban EFCC ya yi karin haske

A wani labari na daban, Abdulrasheed Bawa, shugaban hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ya ce babu wasu rigunan mama da aka samo daga Diezani Alison-Madueke, tsohuwar ministar man fetur, TheCable ta wallafa.

Diezani, wacce ta hanzarta barin kasar nan bayan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya mika mulki ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2015, an zarge ta da sace $2.5 biliyan daga gwamnatin tarayya yayin da ta ke minista, lamarin da ta musanta.

Kara karanta wannan

Rikicin VAT: Gwamnatin Buhari na tunanin sasantawa da Wike da Gwamnonin Kudu ta huta

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel