Hatsarin mota ya lakume rayukan mutum 159, wasu 1,572 sun jikkata a Abuja

Hatsarin mota ya lakume rayukan mutum 159, wasu 1,572 sun jikkata a Abuja

  • Hukumar kare haɗurra ta kasa (FRSC) ta bayyana cewa hatsarin motoci 850 a Abuja ya lakume rayukan mutum 159
  • Kwamandan FRSC na birnin tarayya Abuja, Mista Oga ya kara da cewa wasu 1,572 sun jikkata a tsakanin watan Janairu zuwa Nuwamba
  • Yace rashin sanin dokoki da ƙa'idojin tuki, da kuma fatali da dokokin kan hanya da masu bada hannu ne suke kara ta'azzara lamarin

Abuja - Hukumar kiyaye haɗurra ta kasa (FRSC) ta bayyana cewa aƙalla mutum 159 ne suka rasa rayukansu a hatsarin kan hanya 850 da suka auku a babban birnin tarayya Abuja.

Dailytrust ta ruwaito FRSC ta kara da cewa an samu wannan adadin ne a tsakanin 19 ga watan Janairu zuwa 19 ga watan Nuwamba, 2021.

Kwamandan FRSC reshen Abuja, Ochi Oga, shine ya bayyana haka a wurin taron ƙara wa juna sani da aka shirya wa jami'an Marshal.

Read also

Aisha Yesufu ga majalisar dokoki: Ku tsige Buhari, har 'yan Arewa sai sun ji dadin haka

Jami'an FRSC
Hatsarin mota ya lakume rayukan mutum 159, wasu 1,572 sun jikkata a Abuja Hoto: autoreportng.com
Source: UGC

Mista Oga ya kara da cewa adadin wasu mutum 1,572 ne suka jikkata a tsawon wannan lokacin da ya gabata, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Meke kawo yawaitar hatsari?

Kwamandan ya nuna tsantsar damuwarsa da cewa matukar ba'a ɗauki matakin shawo kan lamarin ba, to nan gaba zai iya taba cigaban tattalin arzikin Abuja.

Bugu da kari, Oga yace ana samun karin yawaitar hatsarin mota a Abuja ne saboda matsanancin gudun direbobi, saba wa dokokin hanya da na tuki da kuma shaye-shaye kafin fara tuki.

Da yake nasa jawabin a wurin taron, kwamandan shiyya na FRSC, Jonas Agwu, yace rashin sanin dokokin tuki ke kara kawo yawan hatsari a kan hanya.

Yace fatali da dokokin hanya da na bada hannu a akan hanyoyin Abuja na daga cikin abubuwan dake kara kawo hatsarin motoci a birnin.

Read also

EFCC na neman wasu 'yan Nigeria 4 ruwa a jallo, ta saki hotunansu

A wani labarin na daban kuma Shekih Ahmad Gumi ya sake jagorantar tawagar Malamai da Likitoci zuwa wani daji a jihar Kogi

Rahotanni sun bayyana cewa Shehin malamin da yan tawagarsa sun je Rugan Fulanin ne domin tallafawa Fulanin ta bangaren duba lafiya.

Shugaban rugar Fulanin, Ardo Zubairu, ya nuna jin daɗinsa da ziyarar malamin, tare da rokon a gina musu makaranta.

Source: Legit.ng

Online view pixel