Abuja: Yadda sojoji suka lakaɗa wa basarake dukan kawo wuka tare da iyalansa

Abuja: Yadda sojoji suka lakaɗa wa basarake dukan kawo wuka tare da iyalansa

  • Wasu sojoji sun afka garin Tunga- Maje da ke yankin Gwagwalada a Abuja ranar Lahadi inda suka dinga dukan Salihu Aliyu, shugaban yankin Galadima da iyalansa
  • An samu rahotanni akan yadda mutane 8 ciki har da wata dalibar kwalejin ilimi dake Zuba, Shemau Salihu duk suka samu miyagun raunuka saboda tsabar duka
  • Yayin bayar da rahoto, Salihu, dan basaraken, yana zaune a kofar gidansu tare da abokansa sojoji suka sauka daga wata mota kirar Hilux suka hau bazgarsu da sanduna

Abuja - Wasu sojoji a anguwar Tunga -Maje da ke yankin Gwagwalada a Abuja a ranar Lahadi sun zane Salihu Aliyu, shugaban yankin Galadima da iyalansa.

Daily Trust ta ruwaito yadda mutane 8 ciki har da wata dalibar kwalejin ilimi ta Zuba, Shemau Salihu, tare da babban dan Galadiman Tungan-Maje, Abdulrahman Salihu suka samu miyagun raunuka sakamakon dukan da suka sha.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Tsagerun yan bindiga sun yi awon gaba da shugaban makaranta, mataimaki da malamai uku

Yayin shaida wa wakilin Daily Trust, Salihu ya ce yana zaune a kofar gidan mahaifinsa tare da wasu abokansa suka ga mota kirar Hilux ta tsaya inda sojoji suka fito da sanduna suka far musu.

Sojoji sun lakaɗa wa basarake dukan kawo wuka tare da iyalansa
Abuja: Yadda sojoji suka lakaɗa wa basarake dukan kawo wuka tare da iyalansa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce sojojin sun raba kawunansu yayin da suke dukansu don sun shiga gidaje 3 ne inda suka dinga dukan mazauna gidajen.

Kafin sannan akwai wata mace da ta zo tare da wani namiji tana nuna ni da hannu tana cewa: “wannan ne dan’uwansa.”

Ya ce yayin da yake tambayar budurwar wanda take nema ne suka fara hayaniya ca ita.

Ya kara da cewa sun kammala sallar isha’i kenan sai ga sojojin sun yi dirar mikiya. A cewarsa, wasu babura har tsayawa suka yi suna kallon yadda ake dukansu.

“Bayan dukanmu har mahaifina su ka kwashe zuwa barikinsu,” a cewarsa.

Kara karanta wannan

Fuskokin wasu kasurguman masu garkuwa da mutane da aka yi ram dasu a jihar Ribas

Galadiman Tungan-Maje ya bayyana yadda sojojin suka cakumi rigarsa bayan ya fito daga masallaci.

“Ina fitowa daga masallaci suka cacumi rigata suka hau dukana da sanda wasu kuma suna harbin iska,” a cewarsa.

Yace sai da suka ja shi a kasa har zuwa wurin motarsa sannan su ka kwashe mutane 7 cikinsu zuwa barikinsu.

Yace bayan sun sakosu sai da ya je asibiti domin a duba lafiyarsa.

Sarkin Tungan-Maje, Alhaji Salihu Isiaku Na’Annabi ya bayyana yadda yana fadar basaraken aka sanar dashi sojojin suna ta dukan Galadima da wasu.

Basaraken ya bayyana yadda yaje bai tarar da su ba sannan yasa dansa ya kira kwamandan barikin wanda yayi alkawarin bincike akan lamarin.

Mataimakin shugaban karamar hukumar Gwagwalada, Alhaji Mohammed Kasim Ikwa, ya tabbatar wa manema labarai aukuwar lamarin inda yace da safe aka kira shi ana sanar dashi cewa jiya lamarin ya faru.

Kwamishinan ‘yan sandan Abuja, CP Sunday Babani, ya nuna rashin jin dadinsa akan lamarin.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke masu garkuwa da mutane 5 a daji bayan an kai musu tsegumi

Yace ya yi bincike inda ya gano cewa wasu sun samu hayaniya ne da wani shine suka yanke shawarar cizguna wa mutanensa.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel