‘Yan ta’addan Boko Haram sun fito da faifan bidiyon wasu mutane 4 da suka fada hannunsu

‘Yan ta’addan Boko Haram sun fito da faifan bidiyon wasu mutane 4 da suka fada hannunsu

  • Yan ta’addan Boko Haram sun wallafa bidiyon da yake nuna wasu mutane da suka yi ram da su
  • Wadannan mutane su hudu sun tabbatar da cewa har yanzu sojojin Boko Haram su na tsare da su
  • Daga cikin su akwai ma’aikacin UNICEF da aka sace a hanyar zuwa Damboa daga birnin Maiduguri

Borno - ‘Yan ta’addan Boko Haram sun fito, sun wallafa bidiyon da ke nuna wasu Bayin Allah da suka yi awon gaba da su a Arewa maso gabashin Najeriya.

A wani gajeren bidiyo da ya shigo hannun Premium Times, wadannan mutane hudu sun bayyana sunayensu, inda suke aiki, wuri da lokacin da aka dauke su.

Wani daga cikin wadanda ya shiga tarkon ‘yan ta’addan, ya bayyana kan shi a matsayin Zakaria Azirkime wanda yake aiki da kungiyar UNICEF ta Duniya.

Read also

Da duminsa: 'Yan bindiga sun sheke maharbi, sun tasa keyar mutum 30 a Niger

Azirkime yace an dauke shi ne a kan hanyar Maiduguri zuwa garin Damboa, har yanzu yana tsare.

Daya cikinsu kuma ma’aikacin hukuma FRSC ne masu kula da tituna na kasa. Wannan mutumi yace ‘yan ta’addan sun kama shi ne a titin Kano-Maiduguri.

Su kuma ragowar sauran mutane biyun sun fada hannun ‘yan ta’addan ne a tsakanin garin Buratai da Buni Yadi da ke Borno da Yobe a Arewa maso gabas.

‘Yan ta’addan Boko Haram sun sace su
Wadanda Boko Haram su ka kama Hoto: www.premiumtimesng.com
Source: UGC

Jawabin wadanda aka dauke

“Salam alaikum. sunana Imranu Mohammed Askira, ni mai kiwon kaji ne, kuma ma’aikacin NDA. Sojojin Khalifa suka dauke mu a hanyar Buratai - Buni Yadi a ranar 21 ga watan Nuwamba, 2021.” - Imranu Mohammed Askira
“Salam alaikum. Sunana Zakariya Ajikime. Ina aiki da UNIEF. Mun bar Maiduguri zuwa Damboa, sai aka kama mu tsakanin Sabon gari da Wajoroko a ranar 3 ga watan Oktoba, 2021…” - Zakariya Ajikime.

Read also

Akwai yiwuwar ayi wahalar fetur a ko ina, NUPENG ta ba Gwamnati wa’adin shiga yajin-aiki

“Salam alaikum. Sunana Mohammed Askira. Na yi aiki da bankin Premier Commercial Bank a Maiduguri. Sojojin Khalifa suka dauke ni a ranar 6 ga watan Nuwamba, 2021, a titin Buratai zuwa Buni Yadi.” - Mohammed Askira.
“Salam alaikum. Sunana Yusuf Nasiru. Ina aiki da hukumar FRSC. Na bar Kano ina zuwa Borno, aka dauke ni a ranar 2 ga watan Nuwamba, 202. Ina tare da su har yanzu.” - Yusuf Nasiru.

An zo taron AFLPM a Abuja

A jiya Aisha Muhammadu Buhari ta tabbatar da cewa Uwargidar kasar Sierra Leone H.E Fatima Maada Bio ta zo Najeriya domin halartar taron da za ayi.

Bayan haka an ji labarin zuwan Mai dakin shugaban kasar Congo Brazzaville, Antoinette Sassou Nguesso babban birnin tarayya Abuja domin taron AFLPM.

Source: Legit

Online view pixel