Jerin matan Shugabannin Afrika 8 da suka zo halatar taron da Aisha Buhari za ta jagoranta

Jerin matan Shugabannin Afrika 8 da suka zo halatar taron da Aisha Buhari za ta jagoranta

  • Ranar Litinin, 22 ga watan Nuwamba, 2021 dinnan ake yin taron iyalin shugabannin kasashen Afrika
  • Manyan matan nahiyar Afrika sun iso Najeriya tun ranar Lahadi domin halartar wannan taro a Abuja
  • Aisha Muhammadu Buhari ta tabbatar da zuwan matan shugabannin Burundi, Sierra Leone, da sauransu

Abuja - A yau Litinin, 22 ga watan Nuwamba, 2021, za ayi taron matan shugabannin Afrika na AFLPM wanda Hajiya Aisha Muhammadu Buhari za ta jagoranta.

Legit.ng Hausa ta samu labari cewa wasu daga cikin matan shugabannin kasashen nahiyar Afrika sun zo da kansu, yayin da wasu suka tura manyan wakilai.

A shafin na ta na Facebook, uwargidar shugaban Najeriya, Hajiya Aisha Muhammadu Buhari ta wallafa hotunan isowar wasu daga cikin manyan bakin taron.

Angeline Ndayishimiye ta na Najeriya

A ranar Lahadi da kimanin karfe 8:00 na dare, Aisha Muhammadu Buhari ta bada sanarwar saukar jirgin saman Misis Angeline Ndayishimiye daga Burundi.

Kara karanta wannan

Aisha Buhari ta karbi bakuncin matan shugabannin kasashen Afrika a wata ziyara

Haka zalika an ji cewa uwargidar kasar Sierra Leone, H.E Fatima Maada Bio ta iso Najeriya domin tun jiya da dare domin halartar taron da za ayi yau a birnin Abuja.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jerin matan Shugabannin Afrika
Iyalai da wakilan wasu shugabannin kasashen Afrika Hoto: @amuhammadubuhari
Asali: Facebook

Duk a shafin na ta, matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta bayyana cewa Mai dakin shugaban Congo Brazzaville, Antoinette Sassou Nguesso ta zo taron.

Wasu kasasshe sun turo wakilai

An kuma ga hoton shugabar Najeriyar da wakilan shugabannin Zimbabwe, Ivory Coast, da Mauritania.

Ministar tsaro, Oppah Muchinguri Kashiri ta wakilci Zimbabwe, yayin da iyalin shugabar Ivory Coast ta turo Ministar sha’anin mata da yara, Toure Nasseneba.

Naha Cheikh Sidiya wanda ita ce Ministar walwala da kananan yara na Mauritania za ta halarci wannan taron na AFLPM a madadin mai dakin shugaban kasar.

Ba a bar matar mai girma shugaban kasar Sao Tome watau Maria de Fatima Vila Nova ba, ita ma tun yammacin Lahadi ta shigo Abuja domin taron shekarar nan.

Kara karanta wannan

Mun fara tattaunawa da Bankin Duniya domin karbo sabon Bashi, Shugaba Buhari

Aminu Ado Bayero ya zama surukin Ummarun Kwabo.

A karshen makon jiya aka ji babban 'Dan Sarkin Kano, Kabiru Bayero zai auri ‘diyar babban attajiri kuma ‘dan kasuwar nan na garin Sokoto, Alhaji Ummarun Kwabo.

Alhaji Kabiru Bayero ya nemi auren Aisha Ummarun Kwabo a gidan gwamnatin jihar Sokoto. Tawagar da aka tura ta nema masa auren ta biya sadakin N250, 000.

Asali: Legit.ng

Online view pixel