Akwai yiwuwar ayi wahalar fetur a ko ina, NUPENG ta ba Gwamnati wa’adin shiga yajin-aiki

Akwai yiwuwar ayi wahalar fetur a ko ina, NUPENG ta ba Gwamnati wa’adin shiga yajin-aiki

  • Nan da makonni biyu Kungiyar NUPENG ta ma’aikatan man fetur da gas na iya tafiya yajin-aiki
  • Shugabannin kungiyar sun fitar da jawabi jiya, inda suka ba gwamnatin tarayya wa’adin kwana 14
  • NUPENG tana kukan akwai wasu ma’aikatanta da suka yi wata da watanni babu albashi a Najeriya

Abuja - Kungiyar ma’aikatan man fetur da gas a Najeriya, ta ba gwamnatin tarayya wa’adin makonni biyu, a cika alkawarun da aka yi wa 'ya 'yanta.

The Cable tace kungiyar ta NUPENG za ta fara yajin-aikin da zai mamaye duk Najeriya, idan ba a dauki mataki a kan duba halin da ‘ya ‘yanta suke ciki ba.

Wannan wa’adi da kungiyar ta bada ya fito ne daga wani jawabi da shugabanta na kasa, Olawale Afolabi da sakatarensa, Olawale Afolabi suka fitar a jiya.

Kara karanta wannan

Yajin aikin ASUU: Kakakin majalisa ya gayyaci ministar kudi, na ilimi da shugaban ASUU

A jawabin na Afolabi da Afolabi, sun ce NUPENG ta cin ma wannan matsayar ne bayan babban taron da suka yi a ranar Alhamis, 11 ga watan Nuwamba.

Daga cikin matakan da aka dauka bayan zaman na makon jiya shi ne dole a biya 'yan NUPENG bashin albashi da duk hakkokin da suke bin kamfanonin mai.

Punch tace shugabannin NUPENG suna kukan rashin biyan ma’aikatunsu albashi. Kamfanonin da abin ya shafa sun hada da NAOC, NPDC da sauransu.

Motar fetur
Motar man fetur Hoto: www.bbc.com
Asali: UGC

Jawabin da kungiyar ta fitar

“Muna bada wa’adin kwanaki 14 da za mu fara yajin-aiki idan ba a kula da walwala da sauran abubuwan da suka shafi ma’aikatanmu ba.” – NUPENG.

Korar da kamfanin Chevron Nigeria Limited ya yi wa wasu ma’aikatan mai ba tare da an biya su hakkokansu ba, yana cikin korafin da NUPENG ta ke yi.

Kara karanta wannan

Manyan gobe: Hazikan matasa 'yan Najeriya 3 da suka kera motocin a zo a gani da kansu

An kori ma’aikatan ne a 2012 saboda sun shiga kungiyar NUPENG. Jawabin yace duk da sun yi shekara 10 zuwa 20 suna aiki, ba a biya su kudin sallama ba.

“Akwai batun ma’aikatan kamfanin PYRAMIDT da ake ta wasa da suka daga hannun wadannan ‘dan kwangila zuwa wannan ‘dan kwangila.”

Sannan akwai ma’aikatan da ke aiki da kamfanin NPDC da ke karkashin NNPC a rijiyar man OML 24 da sun shafe watanni takwas zuwa goma babu albashi.

Bala Mohammed ya soki gwamnatin tarayya

A jiya ne aka ji Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana cewa idan gwamnatin Najeriya ta so, zata iya kawo karshen matsalar tsaro a kasar nan.

A cewar Bala Mohammed, matukar gwamnati za ta iya datse dukkan hanyoyin sadarwa a wuraren da lamarin tsaro ya yi kamari, za a iya magance matsalar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel