Dalla-dalla: Adadin kudaden da jihohin Najeriya suka tara na harajin VAT a watanni 8 na 2021

Dalla-dalla: Adadin kudaden da jihohin Najeriya suka tara na harajin VAT a watanni 8 na 2021

 • An tattara yawan harajin VAT da gwamnatin Najeriya ta tattaro daga jihohi 36 na kasar da babban birnin tarayya
 • A rahoton da muka samo, an bayyana adadin kudin da kowace jiha ta tara a cikin watanni takwas na farkon 2021
 • A baya dai an sha cece-kuce kan batutuwan da suka shafi kasafta harajin na VAT da jihohi ke tarawa da kansu

Najeriya - Daga watan Janairun bana zuwa Agusta, Najeriya ta tara harajin VAT da na biliyoyin Nairori daga dukkan jihohin kasar.

A rahoton da muka samo daga Daily Trust, an bayyana adadin kudaden da kowacce jiha ta kawo a cikin watannin takwas na farkon shearar 2021.

Dalla-dalla: Adadin kudaden da jihohin Najeriya suka tara na harajin VAT a watanni 8 na 2021
Harajin VAT daga jihohin Najeriya | Hoto: The Cable
Asali: Facebook

Duba da alkaluman tara harajin, jihar Legas da babban birnin tarayya Abuja ne suka fi kowacce jiha tara harajin na VAT a watannin.

Kara karanta wannan

Rikicin VAT: Kano kadai ta tara harajin VAT da ya fi na yankin kudu maso gabas a 2021

A cikin wannan rahoton, Legit.ng Hausa ta tattaro daga The Cable yawan kudaden VAT da kowacce jiha ta tara kamar haka:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

 1. Abiya - N2.25bn
 2. Adamawa - N3.97bn
 3. Akwa Ibom - N9.31bn
 4. Anambra - N5.56bn
 5. Bauchi - N5.44bn
 6. Bayelsa - N13.22bn
 7. Benue - N1.42bn
 8. Borno - N3.08bn
 9. Kuros Riba- N1.90bn
 10. Delta - N13.48bn
 11. Ebonyi - N7.21bn
 12. Edo - N9.13bn
 13. Ekiti - N6.2bn
 14. Enugu - N5.19bn
 15. Gombe - N4.44bn
 16. Imo - N1.01bn
 17. Jigawa - N3.05bn
 18. Kaduna - N19.82bn
 19. Kano - N24.41bn
 20. Katsina - N4.64bn
 21. Kebbi - N1.22bn
 22. Kogi - N3.41bn
 23. Kwara - N3.48bn
 24. Legas - N421.20bn
 25. Nasarawa - N2.49bn
 26. Neja - N4.33bn
 27. Ogun - N11.60bn
 28. Ondo - N4.85bn
 29. Osun - N2.07bn
 30. Oyo - N61.05bn
 31. Filato - N5.43bn
 32. Ribas - N92.33bn
 33. Sakkwato - N4.59bn
 34. Taraba - N1.43bn
 35. Yobe - N9.34bn
 36. Zamfara - N762.55m
 37. Babban birnin tarayya - 241.10bn

Kara karanta wannan

COVID-19: Gwamnatin Buhari ta kashe Naira Biliyan 9.9 a kan wanke hannu a 2021

Kano kadai ta tara harajin VAT da ya fi na yankin kudu maso gabas a 2021

A bangare guda, jihar Kano ta lallasa jihohin Kudu Maso Gabashin Najeriya guda biyar gaba dayansu wajen tara harajin VAT na watanni takwas na farkon shekarar nan ta 2021.

Wannan dai na zuwa ne biyo bayan cece-kucen da ake yi kan batun VAT, batutuwan da suka shafi shari'a da kuma tattaunawar siyasa tsakanin gwamnatin tarayya da wasu jihohi, musamman daga kudu.

Wani rahoto na musamman da Daily Trust ta samu ya nuna cewa, bayanan da aka samu na VAT daga Hukumar tara haraji ta FIRS, sun nuna cewa Kano ta tara N24.4b, fiye da kudaden da jihohi biyar suka tara na N20bn.

Asali: Legit.ng

Online view pixel