Boyayyun N19.3bn na albashi: Gwamnatin Kogi ta bai wa EFCC sa'o'i 48 su janye kalamansu

Boyayyun N19.3bn na albashi: Gwamnatin Kogi ta bai wa EFCC sa'o'i 48 su janye kalamansu

  • Gwamnatin jihar Kogi ta bukaci hukumar EFCC da ta fito ta ba ta hakuri tare da Gwamna Yahaya Bello kan alakanta jihar da tayi da N19.3bn
  • A cewar kwamishinan yada labarai da sadarwa na jihar, Kingsley Fanwo, matukar hukumar EFCC ba ta yi haka ba, za ta fuskanci shari'a
  • Har a halin yanzu, gwamnatin jihar Kogi ta ce ba kudin jihar bane EFCC ta kwace tare da mayar da su babban bankin Najeriya

Kogi - Ana cece-kuce tsakanin gwamnatin jihar Kogi da kuma hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, kan boye N19.3 biliyan da gwamnatin ta yi.

Gwamnatin jihar a ranar Lahadi ta kwatanta labarin da "tsabar karya da kuma siyasa" wanda ta ce hukumar yaki da rashawan ta na son bata mata suna ne bayan wasu 'yan siyasa sun yi hayar hukumar, Daily Trust ta ruwaito.

Read also

Gwamnati ta fara rabawa talakawa kudi N1.6bn a jihar Jigawa

Boyayyun N19.3bn na albashi: Gwamnatin Kogi ta bai wa EFCC sa'o'i 48 su janye kalamansu
Boyayyun N19.3bn na albashi: Gwamnatin Kogi ta bai wa EFCC sa'o'i 48 su janye kalamansu. Hoto daga dailytrust.com
Source: UGC

A wata wallafa da gwamnatin jihar ta yi a ranar 19 ga watan Nuwamba, ta bai wa hukumar EFCC wa'adin sa'o'i arba'in da takwas ta janye kalamanta ko kuma ta shirya fuskantar shari'a, kamar yadda ta wallafa a Facebook.

Kwamishinan yada labarai da sadarwa na jihar, Kingsley Fanwo, a wani taron manema labarai a Legas ranar Lahadi, ya jaddada cewa kudin da ake ikirarin an mayar wa babban bankin Najeriya ba na jihar Kogi ba ne.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Amma kuma, gwamnatin jihar Kogi ta ce har yanzu ba a rufe wannan maganar ba kuma ba ta da hannu wurin waskar da kudin tare da boye su inda ta bukaci EFCC da ta fito tare da janye kalamanta da kuma bada hakuri ga gwamnatin da Gwamna Yahaya Bello.

Zuƙi ta malle, ku daina yaudarar ƴan Najeriya, Yahaya Bello ga EFCC kan batun N19.3bn

Read also

Zuƙi ta malle, ku daina yaudarar ƴan Najeriya, Yahaya Bello ga EFCC kan batun N19.3bn

A wani labari na daban, gwamnatin jihar Kogi ta yi martani kan takardar da hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta fitar kan cewa ta mayar da kudi har N19.3 biliyan da gwamnatin ta boye a wani asusun banki zuwa babban kotun Najeriya, CBN.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, Wilson Uwujaren, mai magana da yawun hukumar ya ce hukumar ta mayar da kudin zuwa babban bankin Najeriya.

Amma kuwa, gwamnatin jihar Kogi ta cigaba da musanta boye kudin a wani banki kamar yadda EFCC ta ke zarginta da yi. Jihar Kogin ta ce hukumar so take ta batar da 'yan Najeriya.

Source: Legit.ng

Online view pixel