Zuƙi ta malle, ku daina yaudarar ƴan Najeriya, Yahaya Bello ga EFCC kan batun N19.3bn

Zuƙi ta malle, ku daina yaudarar ƴan Najeriya, Yahaya Bello ga EFCC kan batun N19.3bn

  • Gwamnatin Kogi ta dire gefe tare da karyata rahoton EFCC na cewa jihar ta boye N19.3 biliyan na kudin jihar a wani asusun banki
  • Kwamishinan yada labarai na jihar, Kingsley Fanwo, ya ce babu shakka EFCC ta nuna akwai siyasa a lamarin ta don wannan tsabar sharri ne
  • A cewar kwamishinan, Kogi ta jajanta wa EFCC kan yadda ta zuga karya tun farko sannan yanzu ta zo ta ce ta mayar wa babban bankin Najeriya
  • Kwamishinan Yahaya Bello ya sanar da cewa ba zasu hakura ba, za su dauka matakin shari'a a kan wannan mugun kazafin

Gwamnatin jihar Kogi ta yi martani kan takardar da hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta fitar kan cewa ta mayar da kudi har N19.3 biliyan da gwamnatin ta boye a wani asusun banki zuwa babban kotun Najeriya, CBN.

Kara karanta wannan

Labari da dumi: Mun mayar wa da CBN N19.3bn ta albashin Kogi da Bello ya boye, EFCC

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, Wilson Uwujaren, mai magana da yawun hukumar ya ce hukumar ta mayar da kudin zuwa babban bankin Najeriya.

Zuƙi ta malle, ku daina yaudarar ƴan Najeriya, Yahaya Bello ga EFCC kan batun N19.3bn
Zuƙi ta malle, ku daina yaudarar ƴan Najeriya, Yahaya Bello ga EFCC kan batun N19.3bn. Hoto daga EFCC
Asali: Facebook

Amma kuwa, gwamnatin jihar Kogi ta cigaba da musanta boye kudin a wani banki kamar yadda EFCC ta ke zarginta da yi. Jihar Kogin ta ce hukumar so take ta batar da 'yan Najeriya.

Ta sha alwashin cewa za ta dauka matakin shari'a kan hukumar domin wanke sunan gwamnatin ta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar gwamnatin jihar Kogi, hukumar yaki da rashawan ta fallasa cewa ta na da wata manufa ta siyasa a tattare da ita, Daily Trust ta ruwaito.

A wata takarda da aka bai wa manema labarai a garin Legas, kwamishinan yada labarai da sadarwa na jihar Kogi, Kingsley Fanwo, ya ce gwamnatin za ta shirya martani cikakke ga hukumar "domin tseratar da kanta daga wannan cin fuska da ake yi mata tare da sharri."

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya bi sahun Sheikh Gumi, Ya Bayyana hanyar da Buhari zai bi ya kawo karshen yan bindiga

"Wannan takardar da hukumar ta fitar wa da manema labarai gaskiya cike ta ke da sharri kuma da kokarin saka jihar cikin lamarin da bata da hannu a ciki," yace.
"Muna cigaba da tsayuwa kan gaskiyar mu na cewa jihar Kogi ba ta da wani asusun banki wanda takardar ke magana a kai. Muna jajanta wa EFCC ganin cewa babban aiki ne rufe karyar da suka fara zabgawa tare da yaudarar da suke yi.
"'Yan jihar Kogi da dukkan 'yan Najeriya su tabbatar da cewa za mu ga karshe wannan al'amarin," ya kara da cewa.

Mun mayar wa da CBN N19.3bn ta albashin Kogi da Bello ya boye, EFCC

A wani labari na daban, hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta ce ta mayar da N19.3 biliyan kudin jihar Kogi wanda gwamnatin jihar ta boye zuwa babban bankin Najeriya.

Kara karanta wannan

2022: Kano ta ware miliyan N800 domin magance talauci da rashin aiki a tsakanin mata

Hukumar tun farko ta sanar da yadda mulkin Gwamna Yahaya Bello ya kwashe kudin tare da dankara su a wani asusun banki, Daily Trust ta ruwaito.

Daily trust ta ruwaito cewa, gwamnatin jihar Kogi ta musanta boye kudin inda ta zargi EFCC da zabga karya. Amma a takardar da Wilson Uwujaren, mai magana da yawun hukumar ya fitar, ya ce kudin an mayar da su zuwa babban bankin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel