Jirage kusan 100 da hukumar EFCC ta karbe sun fara tsa-tsa, su na ta rubewa a cikin ruwa

Jirage kusan 100 da hukumar EFCC ta karbe sun fara tsa-tsa, su na ta rubewa a cikin ruwa

  • Lauyoyin hukumar EFCC sun yi nasarar karbe wasu jiragen ruwa bayan an yi ta fafatawa a kotu
  • A halin yanzu wadannan jirage su na cikin wani wulakantancen hali, an bar su tsamo-tsamo a ruwa
  • ‘Yan majalisar tarayya sun zagaya, sun ga yadda gwamnatin tarayya ke asarar kadarori masu tsada

Wasu daga cikin jiragen ruwan da hukumar EFCC ta karbe sun fara nutsewa a ruwa a kasar nan. Jaridar Punch ta fitar da wannan rahoto a makon nan.

Kotu ta ba hukumar ta EFCC damar karbe wadannan jirage na ruwa na wucin gadi ko ma na din-din-din, amma ana ta asara saboda ba a kula da jiragen.

Binciken da jaridar tayi ya bayyana mata cewa gwamnatin tarayya ba ta ware wasu kudi a kasafin kudin Najeriya domin a rika kula da jiragen ba.

Read also

'Yan bindiga sun sace dan uwan hadimin Jonathan da wasu mutum 8 a Kwara

Wata majiya daga majalisar tarayya ta bayyana cewa wannan ya sa sojojin ruwa suka bar jiragen a haka.

‘Yan majalisar wakilan kasar sun ce mafi yawan wadannan jirage suna jihar Legas. A nan ne aka fi yin asarar dukiyoyin da EFCC ta sha wahalar karbewa.

Jirage
Wani katafaren jirgin ruwa Hoto: www.navalnews.com
Source: UGC

Wani kwamiti da aka kafa a majalisar wakilai domin ya binciki duka kadarorin da gwamnatin tarayya ta karbe daga shekarar 2002 zuwa 2020 ya tado batun.

Kwamitin na musamman ya ziyarci duk inda aka ajiye wadannan jirage a ruwa domin ganewa kansa halin da su ke ciki, domin a dauki matakin da ya kamata.

'Yan majalisar tarayya sun koka

Rahoton yace ‘yan majalisar kasar sun yi Allah-wadai da halin da suka samu jiragen a lalace.

“Akwai wasu kadarorin da wasu ne suke kula da su. Amma da yawansu (kadarorin), an rufe su ne kurum a nan. Sun kyale masu aiki a yankin su cigaba.”

Read also

'Yan aware daga Kamaru sun shigo Najeriya, sun kashe mutane, sun kone gidaje

“Abin da ya fi muni shi ne lalacewar da dukiyoyin da aka karbo suke yi. Gidaje na rage daraja, amma ba kamar kayan da ke cikin ruwa ba.” – ‘Dan majalisa.

‘Dan majalisar yace an bar wadannan dukiyoyi suna ta sukurkucewa, suna rage daraja a kullum.

Hadarin mota a Jihar Gombe

An ji cewa an yi wani hadarin mota a Jihar Gombe inda direba, mai dafa abinci da wani ‘Dan Sandan fadar Sarki Tula duk su ka mutu a hanyar Gombe zuwa Yola.

Sarkin Tula, Mai martaba Abubakar Atare Buba II ya ce shi da duka mutanen kasar Tula sun yi rashi, ya yi addu’a Allah ya jikan wadanda suka riga mu gidan gaskiya.

Source: Legit.ng

Online view pixel