Tawagar Sarki tayi hadari a titin Gombe-Yola, mutane sun mutu, wasu su na gadon asibiti

Tawagar Sarki tayi hadari a titin Gombe-Yola, mutane sun mutu, wasu su na gadon asibiti

  • Mutane uku ne ake da labarin sun hallaka a wani hadarin mota da ya rutsa da Sarkin kasar Tula
  • Mai martaba Abubakar Atare Buba II ya rasa direba, ‘dan sanda da mai dafa masa abinci a hadarin
  • Tawagar Abubakar Atare Buba II tayi hadari ta na daf da shigowa garin Kumo a hanyar Gombe-Yola

Gombe - Akalla mutane uku aka tabbatar da sun mutu, wasu da-dama kuma sun jikkata a wani hadari da tawagar Sarkin Tula, Abubakar Atare Buba II tayi.

Jaridar Daily Trust tace direba, mai dafa abinci, da wani jami’in ‘dan sandan da ke aiki da Mai martaba Alhaji Abubakar Atare Buba II duk sun mutu a hadarin.

Mai tuka mai martaba Mai Tula, Danjuma Mohammed da babban mai dafa abinci a fadar Sarki, Mohammed Lawal da Adamu Ibrahim sun rasa ransu a hadarin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun farmaki kwaleji, sun hallaka dalibi da wani lakcara a jihar Legas

Wadannan mutane sun mutu daf da shiga garin Kumo, karamar hukumar Akko, a hanyar Gombe-Yola.

Wasu wanda abin ya faru a gaban idanunsu, sun shaidawa jaridar cewa Danjuma Mohammed da Mohammed Lawal sun rasu nan-take a lokacin da abin ya auku.

Titin Gombe-Yola
Motocin jami'an FRSC a hanya Hoto: thewillnigeria.com
Asali: UGC

Yadda abin ya auku

Hadarin ya auku ne bayan wata motar J5 Peugeot da tayi kokarin shan gaban babbar mota ta kufce, ta aukawa tawagar Sarkin da ke kan hanyar komawa gida.

‘Dan sandan da wannan hadari ya rutsa da shi ya mutu ne a ranar Lahadi, 21 ga watan Nuwamba, 2021, bayan yayi jinya a babban asibitin tarayya na jihar Gombe.

Jaridar The Nation tace wasu mutane uku sun samu rauni a hadarin, kuma su ma suna kwance a asibitin tarayyar ana duba su, an sallami daya daga cikinsu a jiya.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifin tsohon mataimakin gwamnan jihar Imo

Na yi babban rashi - Sarki

Atare Buba II da yake iko a garin Tula da ke karamar hukumar Kaltungo ya yi jimamin rashin da ya yi, ya yi addu’a Allah ya jikan duk wadanda suka rasu a hadarin.

Da aka tuntubi jami’ar FRSC ta jihar Gombe, Janet Kassa, tace ba su san da hadarin ba. Kassa take cewa babu mamaki ‘yan sandan suna da masaniyar hakan ta faru.

Gombe-Yola ta kashe angon Disamba

A daidai wannan hanya ta Gombe zuwa Yola ne aka samu labarin mutuwar wani matashi mai suna Sani Ruba, wanda ya mutu ana saura makonni uku auren sa.

An sa rai cewa marigayin zai auri masoyiyarsa Rafeeah Zirkarnain a ranar 11 ga watan Disamban gobe. Wannan mutuwar ta bar mutane da da-dama cikin juyayi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel