'Yan sanda sun yi ram da farfesa a kan haike wa yarinyar mai gadinsa

'Yan sanda sun yi ram da farfesa a kan haike wa yarinyar mai gadinsa

  • A ranar Lahadi rundunar ‘yan sandan jihar Ebonyi ta kama farfesan jami’a, Felix Anyaegbunam, akan yin lalata da yarinya mai karancin shekaru
  • Anyaegbunam farfesa ne a jami’ar gwamnatin tarayya ta Ndufu-Alike (AE-FUNAI), karamar hukumar Ikwo da ke jihar kuma yana lalata da mai aikin gidansa a kullum
  • Shugaban kungiyar kare cin zarafin jinsi ta jihar, Faithvin Nwancho, ta kai wa ‘yan sanda rahoto akan fyaden da farfesan ya ke yi wa yarinyar wacce take zama da shi kullum

Jihar Ebonyi - Rundunar ‘yan sandan jihar a ranar Lahadi ta kama farfesan jami’a, Felix Anyaegbunam bisa laifin lalata da karamar yarinya, The Punch ta ruwaito.

Anyaegbunam farfesa ne a jami’ar gwamnatin tarayya ta Alex Ekwueme, da ke Ndufu-Alike, (AE-FUNAI), karamar hukumar Ikwo da ke jihar.

Read also

Sanata Walid Jibril: Za mu fatattaki jam'iyyar APC a 2023

'Yan sanda sun yi ram da farfesa a kan haike wa yarinyar mai gadinsa
An kama farfesa a kan haike wa yarinyar mai gadinsa. Hoto: Daily Nigerian
Source: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Vanguard ta bayyana yadda ake zargin farfesan da yi wa wata mai masa hadima a gida mai shekaru 13 fyade, ‘yar asalin karamar hukumar Ezza ta arewa da ke jihar Ebonyi.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ta ce farfesan na hannun hukuma

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Loveth Odah, ta bayyana wa manema labarai ta wani sako na WhatsApp a Abakaliki cewa yanzu haka wanda ake zargin ya na hannun ‘yan sanda.

Kamar yadda kakakin ta bayyana:

“Kwamishinan ‘yan sanda, Aliyu Garba, ya bayar da umarnin yin bincike akan lamarin kwarai yayin da ake jiran ganin sakamakon binciken asibitin yarinyar.”

Shugaban kungiyar dakatar da cin zarafin jinsin jihar (GBV), Faithvin Nwancho, ta kai rahoto ga ‘yan sanda akan fyaden da farfesan ya ke yi wa karamar yarinyar.

Read also

'Yan bindiga sun farmaki kwaleji, sun hallaka dalibi da wani lakcara a jihar Legas

Nwancho ya hori ‘yan sanda da su yi adalci a lamarin

Nwancho ta bukaci ‘yan sanda su kasance masu adalci akan lamarin, inda ta bayyana yadda farfesan ya dirka wa wata yarinya ciki wanda hakan ya yi sanadin barin makarantarta.

A cewarta:

“Wannan farfesan na AI-FUNAJ ya dade ya na lalata da yarinyar mai shekaru 13. Tana zama a gidansa ne kuma kullum sai ya yi lalata da ita.
“Yana kwanciya da ita. Da Ubangiji ya nemi tona masa asiri ne aka sanar damu wannan lamari sannan muka ceci yarinyar. Daga nan muka kai korafi sannan ‘yan sanda suka kama shi.”

'Yan sanda sun yi ram da wasu samari 2 bayan sun datse wa juna hannaye yayin kwasar dambe

A wani labarin, 'yan sanda sun yi ram da samari 2 bisa kama su dumu-dumu da laifin sare wa juna hannaye, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Read also

Taka dokar hanya: An kame baburan 'yan achaba a Legas, an murkeshesu a bainar jama'a

An ruwaito yadda ‘yan sandan su ka kama Adamu Mohammed da Bukar Audu, bayan sun datse wa juna hannaye yayin wani fada da su ka tafka a Garin Alkali, karamar hukumar Dapchi da ke jihar Yobe.

Premium Times ta bayyana yadda Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Dungus Abdulkarim, a ranar Litinin a Damaturu ya bayyana a wata takarda.

Source: Legit.ng

Online view pixel