Jigon APC ya bayyana sirri, ya ce Buhari na goyon bayan shugaba daga yankin Igbo

Jigon APC ya bayyana sirri, ya ce Buhari na goyon bayan shugaba daga yankin Igbo

  • Wani jigon jam'iyyar APC ya bayyana cewa, Shugaba Buhari na goyon bayan mayar da kujerar shugabancin kasar nan kudu
  • Ya bayyana haka ne yayin da yake bayyana kudurin yankin kudu maso gabas na samar da Shugaba daga kabilar Igbo
  • A cewarsa, ya kamata a saki Nnamdi Kanu idan ana son yankin kudu ya zauna lafiya sannan a ba yankin shugabancin Najeriya a 2023

Abuja - Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, wani jigo a jam’iyyar APC kuma Darakta Janar na Voice of Nigeria (VON), Mista Osita Okechukwu, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari a sirrance yana goyon bayan a samar da shugaban Najeriya daga yankin Igbo a zaben 2023.

Da yake magana da manema labarai a ranar Lahadi a Abuja, Okechukwu ya ce shugaba daga ‘yan kabilar Igbo ne zai kawo karshen tashe-tashen hankula da barazanar kungiyar IPOB a yankin Kudu maso Gabas.

Kara karanta wannan

Shugabancin 2023: Ku jira don jin ta bakinsa a watan Janairu - Fashola game da takarar Tinubu

Jigon APC ya bayyana sirri, ya ce Buhari na goyon bayan shugaba daga yankin kudu
Darakta Janar na VON | Hoto: rebenabati.com
Asali: UGC

A cewarsa:

“Shugaban kasa da sauran ’yan Najeriya sun yi shiru suna goyon bayan samar da shugaban Najeriya daga yankin Igbo a 2023, amma sun shuru kuma sun yi watsi da ra’ayin IPOB. Don haka, a karamar fahimta ta, tallafin da IPOB ke ba mu, zai kashe tsuntsaye biyu da dutse daya.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya bayyana cewa wasu masu rike da madafun iko a siyasar Najeriya suna goyon bayan tsayar da shugaban kasa daga shiyyar Kudu Maso Gabas amma suna tsoron ayyukan kungiyar ta IPOB a shiyyar, don haka akwai bukatar kungiyar ta goyi bayan matsayar dattawa kan shugabancin Igbo.

Ya kara da cewa:

“Abinda na fahimta game da fafatukar IPOB shine kawo karshen wariyar da ake wa ‘yan kabilar Igbo. Idan kuwa haka ne, shugaban mu na Najeriya na 2023 na daga yankin Ibo zai kawo karshen yakin basasan. ‘Yan Najeriya na jiran IPOB ta canza salo.”

Kara karanta wannan

Bukatar sakin Nnamdi Kanu babban lamari ne, amma zan yi shawara: Buhari ga Dattawan Igbo

“Ina kuma kira ga IPOB da ta tallafa wa Shugaban Najeriya na tsagin Igbo a 2023. Ina ganin goyon bayan IPOB zai kashe tsuntsaye biyu da dutse daya.
“Ina tare da Ohaneze Ndigbo, fitaccen Lauyan Tsarin Mulki kuma Shugaban Shugabannin Igbo, Farfesa Ben Nwabueze, da masu kishin kasa baki daya wajen yabawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa amincewa da sakin jagoran IPOB da ke rike da shi."

Ya kuma bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya duba batun sakin shugaban kungiyar ta IPOB, Nnamdi Kanu, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Buhari ya shaidawa shugabannin Igbo da suka ziyarce shi a Aso Rock ranar Juma’a cewa zai duba bukatar a saki Kanu.

Rikicin APC: 'Yan sanda sun mamaye sakateriyar jam'iyyar APC a Abuja

A wani labarin, adadi mai yawa na 'yan sanda cikin manyan motocin sintiri hudu ne suka mamaye hanyar shiga da fita a titin Blantyre da ke cikin sakatariyar jam’iyyar APC a Abuja.

Kara karanta wannan

Kungiyar 'Edo Volunteers for Tinubu 2023' tana goyon bayan ƙusan APC a zaben 2023

An tattaro a ranar Laraba cewa ‘yan sandan da jami'an tsaro na DSS suna wurin ne domin dakile yiwuwar tabarbarewar doka da oda.

Wakilin jaridar Punch ya samu labarin cewa jami’an tsaron sun taru ne bayan samun rahotannin tsaro game da shirin zanga-zangar da 'yan APC suka shirya yi na nuna adawa da yadda jam’iyyar ta gudanar da zabuka a taronta na gangami na jihohi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.