Shugaban EFCC ya yanki jiki ya fadi yayin da yake magana a dakin taro
- Shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa ya yanki jiki ya fadi yayin da yake jawabi
- Ministan sadarwa da sauran jiga-jigan gwamnati sun taro shi kana suka fita dashi a dakin taron
- An sanar da cewa, zuwa yanzu shugaban na EFCC ya farfado, amma dai bai dawo dakin taron ba
Abuja - Shugaban Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC), Abdulrasheed Bawa ya yanki jiki ya fadi a bikin ranar kasa ta uku a Banquet Hall Villa, Tribune Nigeria ta ruwaito.
Bawa wanda ke isar da sakon fatan alheri ba zato ba tsammani ya carke, ya koma kan kujerarsa, ya yanki jiki ya zube.
Bawa ya tsaya da magana ya rufe fuskarsa da tafin hannunsa na dama, yana mai cewa,:
"Don Allah, ku gafarce ni, ba zan iya ci gaba ba."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Dijital, Farfesa Isa Pantami, da wasu manyan mutane sun rike shi, bayan wani lokaci, aka yi masa jagora ya fita daga zauren taron.
A cewar rahoton Daily Trust Jagoran Bikin (MC) daga baya ya ba da sanarwar cewa yanayin Bawa ya dan warware.
A cewarsa:
"Ina mai farin cikin sanar da ku cewa Shugaban EFCC a yanzu ya warware."
Amma shugaban da wadanda suka hanzarta fitar da shi har yanzu basu komo cikin zauren ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.
Abun bakin ciki: Shugabar NBA Abuja, Hauwa Shekarau ta rasu bayan yar gajeriyar rashin lafiya
Kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) reshen Abuja ta rasa shugabarta, Hauwa Shekarau a ranar Laraba, 15 ga watan Satumba.
A cewar sakataren NBA reshen Abuja, Prince Adetosoye, Hauwa ta rasu bayan ta yi fama da gajeriyar rashin lafiya, jaridar Punch ta rahoto.
Sanarwar da Adetosoye ya fitar kan wannan babban rashi ya zo kamar haka:
“Cike da bakin ciki da nauyin zuciya nake sanar da rasuwar shugabarmu, wacce ta rasu da safiyar yau, 15 ga Satumba 2021 bayan gajeriyar rashin lafiya.
"Zan yi karin bayani game da tsare-tsare da shirye-shiryen jana'izarta daga baya."
Hauwa ta kasance fitacciyar mai fafutukar jinsi, mai fafutukar kare hakkin dan adam, kwararriyar mai shiga tsakani kuma mai sasantawa, Sahara Reporters ta ruwaito.
Yadda wani mutum ya dirka wa direban keke-napep duka nan take ya mutu
A wani labarin, an zargi wani direban keke-napep mai suna Kola Adeyemi da laifin dukan wani dan uwansa mai keke-napep a Ilorin, babban birnin jihar Kwara.
Daily Trust ta tattaro cewa wanda ake zargin, Kayode Oluwatomi, wanda aka fi sani da “lawyer” ma’aikaci ne na kamfanin tuntuba na BYC da ke yankin Irewolede a Ilorin. An ce ya farma mamacin ne saboda ya bugi abin hawansa ta baya.
Tribune Nigeria ta bayyana cewa, lamarin ya faru ne a ranar Litinin 14 ga watan Satumba da misalin karfe 4:30 na yamma.
Asali: Legit.ng